Ghana ta bi sahun kasashen da za su canja kudinsu

Shugaban Ghana Nana Akufo Addo Hakkin mallakar hoto Sean Gallup
Image caption Kasar Ghana ce kasa ta tara da ta shiga sahun kasashen da suka bayyana aniyar su ta fara amfani da kudin Eco

Ghana ta sanar da kudirinta na shiga sahun kasashen Afrika ta Yamma guda takwas da za su fara amfani da kudin bai-daya na Eco, wanda kudin yuro na Tarayyar Turai zai kasance ma'auni.

Kasashen da suka amince su fara amfani da sabon kudin a 2020 sun hada da Benin da Burkina Fasa da Guinea-Bissau da Code d'Ivoire da Senegal da Togo da Mali da kuma Nijar.

Yawanci kasashen wadanda Faransa ta yi wa mulkin mallaka za su jingine amfani da kudinsu na CFA, yayin da Ghana da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka za ta ajiye amfani da kudin ta na Cedi, ta rungumi kudin bai-daya na Eco.

Yawanci kasashen sun yi amannar cewar rungumar tsarin na amfani da kudin bai-daya zai taimakawa wajen saukaka harkokin cinikayya da samar da tsayayyen tsarin kasuwanci a tsakaninsu.

Har yanzu dai Najeriya na waswasin shiga shirin saboda fargabar rashin tabbas.

Sai dai wasu masana tattalin arziki na ganin yanayin kasuwancin bai-daya a irin yanki na Afirka babban jan aiki ne, musamman shakku da ake nunawa game da sharudda da tabbatarwa da kuma cimma bukatun tattalin arziki a cikin lokaci wajen kafuwar wannan bukata ta su.

Irin wannan bukatar dai ta dauki kungiyar Tarayyar Turai shekaru da dama.

Masana na ganin ga dorewar tsarin, dole sai ya kasance an gudanar da mafi yawancin kasuwancin tsakanin kasashen na Afirka.

Masharhantan na ganin wannan shi ne babban kalubalen da za a fuskanta, domin yawancin kasashen Afirka sun fi hulda ne da kasashen waje maimakon makwabtansu na nahiyar.

Kasuwanci tsakanin kasashen Afirka bai wuce kashi 16 ba duka. A tsakaninsu da kasashen yankin Asiya kuma kashi 51, a Turai kuma adadin ya kai kashi 70.

Hakan ya nuna sabon kudin da kuma niyyar kasuwancin na bai-daya zai iya fuskantar kalubale kafin ya karbu cikin lokaci kankani.

Labarai masu alaka