Masu karbar albashi fiye da daya za su fuskanci shari'a a Zamfara

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle Hakkin mallakar hoto @Bellomatawalle1

Gwamnatin Zamfara ta ce za ta gurfanar da ma'aikatan da ta gano suna karbar albashi fiye da daya a gaban kotu bayan ta kaddamar da bincike domin gano ma'aikatan bogi.

Daga cikin wadanda gwamnatin ta ce bincikenta ya gano har da darakta a ma'aikatar kudi wanda aka dakatar.

Kwamishinan kudin na Hon Rabi'u Garba Gusau, wanda ya jagoranci binciken ya shaida wa BBC cewa akwai wasu daruruwa da aka gano Babban Bankin Najeriya bai san da asusun ajiyarsu ba na banki.

Ya ce adadin ma'aikata 4,972 ne gwamnatin ta dakatar da biyansu albashi wadanda bincike ya gano suna da matsala.

"Masu karbar albashi fiye da daya akwai mutum 109 wadanda kuma ke karbar albshin wadanda da ba su cikin kudin tsarin biyan albashin ma'aikata sun kai mutum 108.

Gwamnatin Bello Matawalle ta PDP da ta gaji gwamnati APC ta Abdul'aziz Yari ta APC ta ce makudan kudi ne ta gano da ake danne wa ta hanyar albashi.

Kwamishinan ya ce idan sun kammala bincike za su mika ma'aikatan zuwa ga hukumar ICPC domin ci gaba da bincike da kuma daukar matakin shari'a akansu.

Labarai masu alaka