Me ya sa ake samun karuwar mutanen da ba sa cin nama?

Young woman sitting holding a bowl full of spinach, rocket and avocado. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutum 600,000 ne ba sa cin nama a Birtaniya a 2018

A sassan Birtaniya, mutane suna kashe kudi wurin sayen kayayyakin abinci da ba nama a ciki sannan kuma nau'o'in abincin da wadannan mutanen ke ci sun yadu a shafukan sada zumunta.

Ganin yadda manyan shaguna suke kawo irin abincin wadannan mutanen, BBC na tambayar ko menene dalilin hakan?

Yawan mutanen da ba sa cin nama ya karu

Irin nau'in abincin bai hada da nama da kifi da kwai da madara ba.

A cewar wani bincike na baya-bayan nan na kungiyar Vegan Society wanda aka gudanar a 2018, akwai kimanin mutum 600,000 da ba sa cin nama a tsibirin Great Britain.

An kididdige cewa wannan adadin ya karu daga 150,000 a 2016 kuma mata sun ninka adadin mazan da ba sa cin nama.

Kusan mutum 360,000 sun bayyana kan su a matsayin wadanda suka zabi tsarin daina cin nama wanda kuma suka tsarawa kansu kin sayen kayan da aka yi da fatar dabbobi.

Shaguna sun bi sahu

Shagunan sayar da kayayyaki a Birtaniya na kawo karin nau'o'in abincin mutanan da ba sa cin nama domin biyan bukatun wani bangare na kwastamominsu.

A 2018, kamfanin Waitrose ya ware wani bangare musamman domin ajiye nau'ikan abincin mutanen da ba sa cin nama a shagunansa sama da 130, yayin da shagon Iceland ya rawaito cewa sayen irin abincin wadannan mutanen ya karu da kashi 10 cikin dari a shekarar da ta gabata.

Da yawan kamfanonin da ke sarrafa abinci, daga Greggs zuwa McDonalds da kuma Burger King zuwa KFC, sun kaddamar ko sanar da bijiro da tsarin sayar da abincin mutanen da ba sa cin nama a Birtaniya.

Kasuwar sayar da abincin da ba nama a ciki a Birtaniya ta samu £740m a 2018, a cewar masu bincike a Mintel.

Kudin ya karu ne daga £539m shekara uku da suka gabata.

Masu son abincin da ba nama a ciki na karuwa yayin da ake sa ran kudaden da dillalai ke samu za su karu zuwa £658m nan da 2021.

Shin akwai abin da ke tasiri kan abin da muke ci?

Kafafen sada zumunta suna da rawar takawa a karuwar masu bin tsarin cin abincin da ba nama a cikinsa.

Fitattun mawaka irin su Ariana Grande da Miley Cyrus da Ellen De Generes na daga cikin mutanen da suka shahara kuma ba sa cin nama yayin da mutum sama da miliyan 87 suka wallafa sako a shafin Instagram kan maudu'in #Vegan.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Batun kin cin abinci maras nama babban maudu'i ne - yawan mutanen da suke bincike kan batun a fadin duniya a Google shi ma ya karu a baya-bayan nan.

Google na amfani da wata lamba cikin 100 wajen gano masu sha'awar abu. A shekarar 2009, kalmar "veganism" tana da matukar farin jini wadda ta yi tashe sau 33 kawai amma ya karu zuwa 100 cikin shekara 10 bayan haka.

Abu uku da aka fi neman karin haske a kansu game da maudu'in a Birtaniya na neman sanin ko me kalmar veganism take nufi da dorewarta da kuma yadda take shafar sauyin yanayi.

Giles Quick, wani daraktan bincike a Kantar Worldpanel ya ce "kasuwar sayar da abincin da ba nama ta samu gagarumin sauyi cikin shekara shida ko bakwai da suka gabata - yanzu abu ne da ya zama na kowa.

"Kafafen sada zumunta sun taimaka wajen kara karbuwar tsarin a zukatan mutane. Mutane sun daina daukarsa a matsayin abincin rana kadai ko na dare ko na kwana daya."

Tsarin rashin cin ganyayyaki na lokaci zuwa lokaci ko veganism a turance, yana samun karbuwa sosai.

A cikin Janairun 2019, mutum 250,000 sun yi alkawarin komawa tsarin cin abincin da ba nama a farkon watan shekarar, a ƙarƙashin gangamin Veganuary.

Gangamin wanda aka kaddamar a Birtaniya a 2014 wanda kuma ya samu goyon baya a kafafen sada zumunta, ya kara karfafa wa mutane gwiwa kan su gwada cin abincin da ba nama.

Me ya sa mutane suke komawa kan wannan tsari?

A cewar masu nazari, matasa mata na jan ragamar tsarin na cin abincin da ba nama.

Akwai wasu dalilai da suka sa aka samu karin mutanen da ba sa cin nama.

Kimanin kashi 49% na mutanen da ke sha'awar rage yawan cin nama sun ce za su yi haka ne saboda lafiyarsu a cewar wani bincike da aka yi kan sama da mutum 1,000 a tsibirin Great Britain, a cewar kamfanin binciken Mintel.

Batun rage kiba da kula da walwalar dabbobi da matsalolin muhalli su ma wasu manyan abubuwa ne da ka iya jan hankalin mutane ga shiga tsarin.

Yayin da ake samun karuwar mutane da ke karbar wannan tsari, tsarin rashin cin ganyayyaki na lokaci zuwa lokaci na iya komawa tsarin din-din-din.

Labarai masu alaka

Karin bayani