Trump ya cancanci yabo a kisan Soleimani - Netanyahu

Benjamin Netanyahu

Asalin hoton, EPA

Firai ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi maraba da harin da Amurka ta kai wanda ya yi sanadiyyar kashe Soleimani.

Benjamin Netanyahu ya ce Donald Trump ya 'cancanci yabo kan mayar da martanin gaggawa mai karfi kuma yadda ya dace'.

"Isra'ila na tare da Amurka a kokarin samar da zaman lafiya da tsaro da kuma kokarin kare kai,"

Mista Netanyahu ya kuma kara da cewa Amurka na da 'yancin kare kanta.

"Qassem Soleimani ne ya kitsa kisan 'yan Amurka da kuma karin wasu mace-mace. Yana kitsa karin wasu hare-haren irin wadannan."

Benjamin Netanyahu ya koma Isra'ila daga wata ziyara da yake yi a Girka jim kadan bayan harin na Amurka.