Qasem Soleimani: Ya ya karfin sojin Iran ya ke?

A woman looks at missiles on display during a street exhibition in Tehran, Iran Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Iran's missile capabilities are a key part of its military prowess

Iran ta yi alkawarin rama kashe mata janar din soji kuma babban kwamanda da Amurka ta yi a wani harin sama a filin jirgin saman birnin Baghadaza na kasar Iraki.

Jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei, ya ce "ramuwa mai tsanani na jiran" wadanda suka kashe janar Qasem Soleimani.

Shin me kuka sani game da karfin sojin kasar?

Girman rundunar sojin Iran

Iran na da sojoji kusan 523,000 a rundunoni daban-daban, kamar yadda cibiyar binciken dabaru na kasa da kasa da ke Birtaniya ta bayyana.

Kasar na da karin wasu dakaru 20,000 a rundunarta ta sojin ruwan dakarun juyin-juya halin Musulunci wato IRGC.

Rundunar ce ke yin sintiri da jiragen ruwan soji a mashigin Hormuz, inda aka yi ta artabu da jiragen mai na kasashe a shekarar 2019.

IRCG ce kuma ke kula da rundunar sa-kai ta Basij da ke taimakawa wajen murkushe masu tayar da kayar baya a cikin kasar.

Runudanar Basij na da dubban dakaru da ma'aikata.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption IRGC na da sojojin sama da na ruwa kuma ita ke kula da muhimman makaman Iran

Shekara 40 da suka wuce ne aka kafa runduar IRGC domin kare tsarin Musulunci a kasar.

Rundunar ta samu ikon zama wani muhimmin bangare na harkokin soji da siyasa da tatalin arzikin Iran.

Duk da karancin dakarunta idan aka kwatanta da rundunar tsaron kasar, ana ganin IRGC a matsayin sashen soji mafi karfin iko a Iran.

Aikin soji a kasashen ketare fa?

Bataliyar Quds wadda marigayi Soleimani ya jagoranta ce ke gudanar da ayyukan IRGC na sirri a kasashen ketare.

Bataliyar mai karfin soja 5,000 na gudanar da ayyukanta ne kai-tsaye karkashin jagoran addinin kasar wato Khamenei.

An tura wasu sojojin bataliyar a matsayin masu bayar da shawara ga sojojin shugaba Bashar al-Assad na Syria da mayakansa kan 'yan Shi'a da ke tare da su.

A Iraki kuma rundunar ce ta taimaka wa jami'an tsaron farin kaya murkushe kungiyar IS da mayakanta.

Amma gwamnatin Amurka na zargin ayyukan rundunar ya hada da samar da kudade da horo da makamai da kayan aiki ga kungiyoyin da Amurkan ke gani a matsayin 'yan ta'adda a Gabas ta Tsakiya.

Kungiyoyin sun hada da Hezbollah ta kasar Lebanon da kungiyar jihadin Musulunci ta Falasdinu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rundunar IRGC ta taba tsare wani jirgin mai na Birtaniya a mashigar ruwan Hormuz a 2019

Matsaloli da takunkumin karya tattalin arziki sun kawo wa kasar tazgaro wurin sayo makamai. Kasar na da karancin makamai idan aka kwatanta da wasu kasashen yankin.

Yawan makaman da kasar ta saya daga 2009 zuwa 2018 bai fi kashi 3.5% na makaman da Saudiyya ta saya a tsawon lokacin ba, a cewar cibiyar binciken zaman lafiya ta Stockholm.

Galibin makaman tana sayo su ne daga Rasha, ragowar kuma daga China.

Shin Iran na da makami mai linzami?

Kwarai kuwa - makamai masu linzami da Iran ta mallaka shi ne babban karfinta na soji, duba da karancin karfinta na sojin sama idan aka kwatanta da manyan abokan gabanta irin Isra'ila da Saudiyya.

Rahoton ma'aikatar tsaron Amurka ya ce Iran ce mafi karfin makamai masu linzami a Gabas ta Tsakiya.

Makaman a cewar rahoton sun hada da masu cin gajere da kuma matsakaicin zango.

Amurka na ganin Iran na gwajin fasahar sama jannati ne domin kera makami mai linzami da ke iya keta tsakanin nahiyoyi ko ma fiye da haka.

Iran ta dakatar da shirinta na makamai masu cin dogon zango saboda yarjejeniyar 2015 da ta kulla da wasu kasashe game da shirinta na nukiliya.

Daga baya ta ci gaba da kera makaman sakamakon rashin tabbas da ke tattare da yarjejeniyar.

Duk da haka Iran za ta iya kai hari da makaman nata masu cin gajere da matsakaicin zango zuwa cikin kasar Isra'ila da Saudiyya da sauran kasashen yankin Gulf.

A watan Mayun shekarar da ta gabata ne Amurka ta girke na'urar kakkabo makaman abokan gaba a Gabas ta Tsakiya sakamakon nuna yatsa tsakaninta da Iran.

Makamin na iya kakkabo jiragen yaki da rokoki da makamai masu linzami da abokan gaba suka harba a sararin samaniya.

A watan Yunin 2019 Iran ta kakkabo wani jirgin sintiri maras matuki mallakar Amurka bisa hujjar cewa ya keta hurumin sararin samaniyar kasar a mashigin Hormuz.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Amurka na zargin Iran da bayar da jiragen yaki marasa matuka ga 'yan tawayen Houthi na Yemen

Wakilin BBC kan harkokin tsaro da diflomasiya Jonathan Marcus ya ce shirin Iran na jirage marasa matuka ya hada da sayarwa ko bayar da fasahar ga kawayenta ko wakilanta a yankin.

A 2019 wasu hare-haren da aka kai da irin jiragen sun lalata manyan matatun mai na Saudiyya guda biyu.

Amurka da Saudiyya suna zargin Iran da kai harin, amma ta musanta, inda ta dora laifin a kan 'yan Houthi na Yemen da suka dauki alhakin hare-haren.

Shin Iran na da fasahar intanet?

Bayan harin intanet da aka kai wa tashar nukiliyarta a 2010 kasar ta karfafa fasaharta ta intanet.

Ana tunanin IRGC na da runduna ta musamman kan harkokin intanet da ke yi mata ayyukan leken aikin leken asirin kasuwanci da harkokin soji.

Rahoton da rundunar sojin Amurka ta fitar a 2019 ya zargi Iran da kokarin kaddamar da harin leken asiri ta intanet a kan kamfanonin tsaro da na jiragen sama da na makamashi da na albakatun kasa da na sadarwa a fadin duniya.

Labarai masu alaka