Yadda 'yan gida daya ke buga garaya don fadakarwa
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda matasa 'yan gida daya ke kada garaya a Kaduna

Ku latsa wannan hoton da ke sama domin kallon bidiyon

Usman Gashash dan shekara 13 ne da ke buga garaya da manufar fadakar da al'umma.

Usman kan yi kidan gargajiya irin na Buzaye tare da 'yan uwansa 'yan mata biyu da namiji daya.

Suna yin kidin ne don fadakarwa game da irin matsalolin da al'umma ke fuskanta kamar sauyin yanayi da cututtuka da rigakafi da dai sauransu.

Burin Usman shi ne ya shahara a Afirka nan da shekaru biyar masu zuwa.

Bidiyo: Fatima Othman

Labarai masu alaka