Ra'ayin masu sharhi kan takun saka tsakanin Iran da Amurka
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ko Amurka za ta janye sojojinta daga Iraki?

Latsa alamar lasifika domin sauraron Mohammed Qadm Isah

Tun dai bayan da 'yan majalisar dokokin Iraki su 170 ba tare da ragin daka ba suka amince da ficewar sojojin Amurka daga Iraki, masana ke ta tofa albarkacin bakinsu kan yiwuwar hakan ko akasi.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kakaba wa Iraki takunkumi bayan da majalisar dokokin Irakin ta amincewa da korar sojojin Amurkar fiye da 5000 da ke kasar.

"Muna da sansanin sojoji mai matukar tsada da ke can. Mun kashe biliyoyin daloli wajen gina shi. Ba za mu fice daga kasar ba har sai sun biya mu abin da muka kashe."

Ana ci gaba da samun tankiya tsakanin Iran da Amurka tun bayan kashe janar Qasem Soleimani da Amurkar ta yi ranar Juma'a a birnin Bagadaza.

Kasar Iran dai ta sha alwashin daukar "fansa"

Soleimani, mai shekara 62 na jagorantar dakarun kasar ta Iran a samame daban-daban a yankin Gabas ta tsakiya, inda Amurka take daukar sa a matsayin "dan ta'adda".

Tuni dai aka yi jana'izar Soleimani a kasarsa wato Iran inda 'yan kasar suka yi dandazo a titunan kasar da sanyin safiyar ranar Litinin.

Labarai masu alaka