Rahama Sadau na tara wa almajirai kayan sanyi

Rahama Sadau Hakkin mallakar hoto Instagram Rahama Sadau
Image caption Rahama Sadau ta ce tana so ta ragewa almajirai radadin sanyin da suke fama da shi

Yayin da al'umma a kasashen Afirka ta yamma musamman Najeriya ke fama da matsanancin sanyi da masana yanayi suka ce an yi shekaru ba a fuskanci irinsa ba, wasu fitattun mutane a Najeriyar da kungiyoyin sa kai sun yunkuro domin tallafawa marasa galihu musamman almajirai wadanda ba su da halin kare kansu daga yanayin hunturun da ake ciki.

Sanyin bana ya zo da ba-zata kasancewar lamarin ya shafi wuraren da ba su saba fuskantar matsanancin sanyin ba.

Fitacciyar tauraruwar Kannywood mai yawan janyo ce-ce ku-ce Rahama Sadau ta kaddamar da wani asusu na tara kayan sanyi da za a rabawa almajirai a wasu jihohin arewacin Najeriya.

Jarumar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa za a raba kayan da aka tara ne a jihohi kamar Kaduna da Katsina da Jos da Bauchi da Kano da ma wasu da dama.

"Ba za mu iya taimakon kowa ba, amma kowa daga cikinmu zai iya taimakawa wani," a cewar Sadau.

Ta kara da cewa, "babu wata mafificiyar hanya da za a taimaki almajiri fiye da samar musu kayan da za su rage musu jin sayi, ko kuma kudi domin tallafa musu."

Ta yi kira ga jama'a kowa ya hada hannu domin taimakawa almajiran, wadanda ta ce bai kamata a yi watsi da su ba.

Baya ga tufafi, Rahama Sadau ta ce za ma a iya ba da tallafin kudi.

Ba dai wannan ne karon farko da taurarin Kannywood suka fara tallafawa marasa galihu a cikin al'umma ba.

Taurari irin su Hadiza Gabon da Masura Gabon da Aisha Tsamiya da wasu taurarin suna tallafawa marasa karfi a cikin al'umma.

Ba Rahama Sadau ba ce kadai

Masana dai sun ce sanyin na bana na karuwa ne saboda gudun iskar da ke tasowa daga arewa maso gabas mai kunshe da laima ya karu, inda a wasu lokuta har takan kai gudun kilomita 100 cikin sa'a daya.

Yanayin sanyin dai ya sanya mutane bayyana ra'ayoyinsu kan halin da suke ciki abin da kuma ya sa kungiyoyi da wasu fitattun mutane suka dauki ragamar kaddamar da shirin karbar gudummawar tallafawa marasa galihu.

Wani almajiri ya shaidawa BBC Hausa cewa tun da aka fara sanyi nan sau daya ya yi wanka, yayin da wani kuma ya ce gabobinsu suna rikewa idan sun tashi da safe saboda tsananin sanyi da kuma rashin abin rufa.

Wani malamin makarantar allo ya ce almajiransa na kwana ne a rumfar kwano da aka rufe samanta, amma ta gefe da gefe kuma take a bude.

Irin wannan yanayi da ake ciki ya sa tuni wasu mutane musamman shahararru a shafukan Sada zumunta suka kaddamar da irin wannan yunkurin na tallafawa almajirai da abin rufa.

Nana Asma'u Gwadabe, daya ce daga cikin 'yan sa kan da suke samar wa Almajirai gudunmuwar barguna, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Instagram.

Nana ta shaidawa BBC sun ba da barguna 500 sannan akwai wasu karin bargunan 1,000 da za su ci gaba da rarraba wa almajiran domin su samu abun rufa a halin da ake ciki na matsanancin sanyi.

Shi ma, wani mai amfani da shafukan sada zumunta Abubakar Widi Jalo ta shafinsa na Facebook ya kirkiri maudu'in #KeepTheVulnerableWarm inda mutane suke tururuwar bayar da gudummawarsu.

Shirin na #KeepTheVulnerableWarm, a cewar Jalo ya samu gudummawar sama da naira miliyan guda wanda da kudin ne aka sayi barguna da rigunan sanyi domin rarrabawa mabukata a jihohin Kano da Jigawa da Kaduna da Yobe da Maiduguri da Jos da kuma Bauchi.

Baya ga wadannan, akwai kuma zaurukan WhatsApp da dama dake tattara irin wadannan gudunmuwa ga almajirai domin rage musu tsananin sanyi a wannan lokaci na hunturu.