Yadda Iran ta kai wa sojojin Amurka hari a Iraki
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda Iran ta kai wa sojojin Amurka hari a Iraki

Latsa bidiyon sama domin ka kallo

Rundunar Musulunci ta juyin-juya hali ta Iran (IRGC) ta bayyana cewa ta dauki fansa a kan Amurka kan kisan Janar Qasem Soleimani, babban kwamandan rundunar Quds.

Amurka ta kashe shi ne a Iraki a filin jirgin sama na Bagadaza cikin wasu ayarin motoci.

Ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif ya fitar da sanarwa a Twitter, yana cewa harin na kariyar kai ne tare da nesanta harin da nufin kara dagula al'amura domin afkawa cikin yaki.

Shugaba Trump ma ya wallafa a Twitter cewa "komai lafiya lau", inda ya kara da cewa ba su kai ga tantance ko an samu hasarar rayuka ba.

An kai harin ne jim kadan bayan binne Soleimani.

An kai hari na biyu a Irbil bayan an kai na farko da makamin roka a Al Asad, kamar yadda kafar Al Mayadeen ta ruwaito.

Tun da farko shugaba Trump ya ce janye dakarun Amurka zai kasance mataki mafi muni ga Amurka.

Kalamansa na zuwa bayan wata wasika da rundunar sojin Amurka ta ce an tura bisa kuskure ga Firaministan Iraki, matakin da majalisar Iran ta amince kan bukatar janye dakarun na Amurka.

Amurka tana da yawan dakaru 5,000 a Iraki.

Kisan Soleimani a ranar 3 ga Janairu ya kara tsamin dangantaka tsakanin Iran da Amurka.

Miliyoyin Iraniyawa ne suka fito kwansu da kwarkwata domin jana'izar babban kwamandan na Iran da Amurka ta kashe, inda suke ta furta kalamai na barazana ga Amurka da kuma Trump

Akalla mutum 50 ne suka mutu yayin turmutsutsin jana'izar Soleimani.

Labarai masu alaka