Ko kida na kara kuzari yayin motsa jiki?

Woman with earphones Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dangane da rage kiba, daya daga cikin mafi karbuwar abubuwan da mutane suka kuduri yi a sabuwar shekara shi ne "yin atisaye sosai".

Ko da yake kowane irin nau'in atisaye ya fi zama haka nan kawai, yin atisaye cikin hanzari na da amfani musamman ga zuciya da kuma kwakwalwa.

A don haka idan kana daya daga cikin miliyoyin mutanen da suka kuduri wannan anniyar ta motsa jiki sosai a wannan shekarar, to watakila hadawa da waka mai kida sosai zai iya taimakawa wajen cimma jijjiga jikin sosai.

A wani gwaji da aka yi na "Trust Me I'm A Doctor", wato ku yarda da ni, ni likita ne, mun duba, kuma mun ga hakan zai yi aiki.

Ba kamar tafiya a hankali ba, tafiya da sauri ya fi taimakawa wajen aikawa da jini zuwa kwakwalwar mutum kuma yasa jikin mutum ya saki kwayoyin halittar BDNF wato (kwayoyin da ke taimakawa kwakwalwa wajen tunani ko tuna abubuwa). Kwayoyin BDNF na taimakawa kwakwalwa wajen samar da sababbin kwayoyin halitta, abin da ba shakka yake da amfani yayin da kake kara tsufa.

Akwai yiyuwar masu tafiya da sauri za su yi tsawon rai fiye da wadanda ke tafiya a hankali.

A wani bincike da aka gudanar na fiye da mutum 50,000 na 'yan Birtaniya da ke yawan tafiya a kasa na Mujallar "British Journal of Sports Medicine", wato mujallar masu motsa jiki don neman lafiya na Birtaniya, ya gano cewa wadanda suka ce suna tafiya da sauri na da yiyuwar samun karin tsawancin rayuwa da kashi 24 cikin 100 fiye da wadanda suka ce suna tafiyarsu a hankali.

Sai dai, abu mai wuya ne a ce an gano dalili da kuma illar hakan daga wannan binciken - saboda yana iya yiyuwa mutanen da ke tafiyar kafa da sauri suna lafiya ne kawai.

Shekara biyu baya da suka wuce, ina cikin wadanda suka gudanar da irin wannan gwaji da Rob Copeland, Farfesa a kan harkokin motsa jiki da lafiya da ke jami'ar Sheffield, inda muka dauki wata kungiyar ma'aikata da ke yawan zama, wadanda muka sa suyi tafiya taku 10,000 ko kuma abin da suka kira "Active 10" wato (wata manhaja da ke taimaka maka wajen komawa ka samu lafiya kyauta).

An saka kungiyar na "Active 10" su sanya tafiya da sauri na minti goma a kullum, a maimakon yin tafiya haka nan kawai.

Mun gano cewa idan batun samun lafiya ne, tafiya da sauri na lokaci kadan yafi alfanu da kuma saukin tafiyarwa, a maimakon kokarin cimma taku 10,000.

Labarai masu alaka