IS na murna da kisan Soleimani - Amurka

  • By Jeremy Bowen
  • Middle East editor, Baghdad
Shugaban mayakan Iraki Abu Mahdi-al-Muhandis shi ma ya rasa ransa a harin da ya kashe Qasem Soleimani

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaban mayakan Iraki Abu Mahdi-al-Muhandis shi ma ya rasa ransa a harin da ya kashe Qasem Soleimani

Matakin da shugaban Amurka Donald Trump, ya dauka na kisan Janar Qasem Soleimani, shugaban rundunar Quds ya bar baya da kura. Daya daga cikinsu shi ne yaki da masu ikirarin jahadi da ba a gama ba.

Da gaggawa gamayyar masu yaki da masu ikirarin jahadi wadda Amurka take jagoranta ta tsayar da ayyukanta a Iraki.

Amurka da abokan kawancenta sun bayyana cewa aikinsu a yanzu shi ne su kare kansu. Daga mahangar soji, kila ba su da wani zabi.

Iran da mayakan da take taimaka wa a Iraki sun sha alwashin daukar fansa kan kisan da Amurka ta yi wa Soleimani da jirgi marar matuki da makami mai linzami a Bagadaza a ranar Juma'a.

Wannan ya sanya dakarun Amurka da kawayenta a cikin mawuyacin hali a Iraki.

Wannan kuma ya yi wa IS dadi. Za kuma ta yi kokarin farfadowa daga bugun da aka yi mata lokacin da aka ruguza mata daula.

Ya kuma yi wa masu tsautstsauran ra'ayi raddi kan kudurin da majalisar Iraki ta amince da shi kan cewa Amurka ta gaggauta fita daga kasarsu.

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto,

Dakarun Amurka da na Turai sun horas da sojojin Iraki kuma sun ba su shawara a kan yadda za a yaki IS.

Kungiyar IS ta nuna jajircewa tsawon shekaru da dama. Ta sake kafa kanta daga ragowar kungiyar al-Qaeda da ta rushe a Iraki.

A 2016 da 2017, an bukaci a yi wani babban aikin soji domin kawo karshen IS a wasu yankunan Iraki da kuma Syriya.

An kashe mayaka da yawa masu ikirarin jihadi, wasu kuma an kulle su gidan yari. Amma hakan bai kawo karshen kungiyar ba.

Iraki na da rundunar sojoji da 'yan sanda na musamman wadanada Amurka da Turawan yamma suka horas wadanda suke yakin IS.

Tun bayan kashe Soleimani, Amurka da Denmark da kuma Jamus sun dakatar da duka ayyukansu.

Jamusa ta janye masu horaswa nata zuwa kasashen Jordan da kuma Kuwait.

Dakarun Iraki ne ke daukar hadarin yaki da IS. Suna bukatar horo da kuma kayan yaki daga dakarun Amurka. Amma su yanzu suna cikin sansaninsu a zaune.

Asalin hoton, IS propaganda

Bayanan hoto,

Wasu maykan IS na ci gaba da kai hare-hare a Iraki.

Mayakan IS suna na abin da za su yi murna a kai. Lokacin da Trump ya kashe Soleimani sun sa mu kyauta daga makiyansu. Shugaban Amurka na taimaka masu.

A 2014, masu ikirarin jihadi sun kai hare-hare inda suka amshe kasashe a cikin Iraki, harda Mosul , birni na biyu mafi girma a Iraki.

Babban malamin Shi'a a Iraki Ayatollah Ali al-Sistani, ya nemi a dauki makamai a yaki mabiya sunni a kasar.

Matasan 'yan shi'a sun amsa kiran dubunnansu. Kuma Soleimani da rundunarsa ta Quds sun taimaka kwarai wajen gyarasu. Mayakan ba su da tausai. Makiyan IS ne sosai.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Kungiyar mayakan Shia ta Popular Mobilisation ta taka muhimmiyar rawa wajen yaki da IS

A yanzu kungiyoyin masu samun goyon bayan Iran an saka su cikin dakarun sojin Iraki a wata runduna mai suna "Popular Mobilisation". Manyan mayakan sun zama 'yan siyasa masu karfin fada a ji.

Bayan 2014, Amurka da mayakan na yakin makiya daya ne. Amma yanzu mayakan za su koma kan turbarsu ta yaki da Amurka wadda ta mamaye musu kasa a 2003.

Sun kashe sojojin Amurka da yawa da taimakon horon yakin da Soleimani ya ba su. Wannan shi ne dalilin da ya sanya shugaba Trumpp ya bayar da umarnin kai harin makon da ya wuce.

Tun da Trump ya fita daga yarjejeniyar Nukiliya da Iran a 2018, Amurkawa da Iraniyawa suka kama hanyar yaki.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga sun kai wa ofishin jakadancin Amurka hari a Bagadaza bayan da ta kashe wasu mayaka a wani hari

Kafin kisan Soleimani, wasu mayakan shi'a na kai wa dakarun Amurka hari.

Wani hari da aka kai a Disamba a wani sansanin soji a arewacin Iraki wanda ya kashe wani ma'aikacin Amurka, ya samu ramuwa ta jirgin sama inda aka kashe mayaka 25 na wata kungiya mai suna Kataib Hezbollah.

Shugabansu Abu Mahdi al-Muhandis ya gana da Bagadaza a filin jirgin sama na Bagadaza, wanda aka tarwatsa tare da shi cikin mota a tare.

Tarihi ya nuna cewa masu ikirarin jihadi na ci gaba ne idan za su iya amfani da damar da ke akwai cikin rudani.