Masu shigo da shinkafa ne ke hayar masu garkuwa da jama'a a Katsina - Masari
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Mun san masu gayyato mana barayi '

Latsa alamar lasifika domin sauraron Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya shaida wa BBC cewa yana zargin wasu mutane a jihar sun rungumi wata halayya ta gayyatar masu garkuwa da mutane zuwa cikin gari domin sace jama'a.

Gwamna Masari ya bayyana cewa mazauna garuruwan da ke kan iyakar Najeriya da Nijer ne suka fi yin wannan ta'ada musamman mutanen garin Jibiya.

Ko a ranar Alhamis sai da gwamnan a cikin wani bidiyo wanda yake ta karakaina a shafukan sada zumunta, ba tare da kumbiya-kumbiya ba ya kama sunan mutanen Jibiya inda ya ce su ne ke kara lalata harkar tsaron garunsu da kansu.

Daga karshe Masari ya jaddada cewa shirin sasanci tsakanin gwamnati da al'umma da masu garkuwa da mutane da ke zaune a cikin daji na nan daram, inda ya ja hankalin masu cewa shirin ya wargatse.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da wasu jami'an kwastam guda biyu a wani shinge da ke kauyen Dan-bedi a yankin karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina mai iyaka da jamhuriyar Nijar.

Batun hare-hare da sace jama'a dai ya zama ruwan dare a jihar Katisna, inda da wuya rana ta fito ta fadi ba tare da samun wani gari ko kauyen da aka samu masu satar jama'a suka far wa ba.

A cikin 2019 ne dai gwamnatin jihar ta Katsina ta bullo da shirin tattaunawa da masu garkuwa da jama'a da satar shanu.

Labarai masu alaka