Rashin lafiyar alkali ya kawo jinkiri ga hukuncin zaben gwamnoni

BBC

Kotun Kolin Najeriya ta daga zamanta da ta fara yi a ranar Litinin 13 ga watan Janairun 2019.

Kotun dai da fara zaman nata ne domin yanke hukunci kan kararrakin zabe da suka hada da na jihohin Kano da Sokoto da Bauchi da Imo da Filato da Benue.

Jim kadan bayan kotun ta fara zamanta sai ta tafi hutu bayan ta fara da shari'a kan zaben Kano tsakanin dan takarar APC Abdullahi Umar Ganduje da kuma na PDP Abba Kabir Yusuf.

Bayan alkalan sun shafe sama da mintuna 45, sai suka aiko da cewa daya daga cikinsu ba shi da lafiya wanda hakan ya sa kotun da dage zamanta.

A wannan dalili ne ya sa kotun da dage zamanta zuwa ranar Talata 14 ga watan Janairun 2020.

Ma'aikatan kotun sun shaida wa BBC cewa hukunce-hukuncen da kotun za ta yanke sun yi yawa, kuma wasu hukunce-hukuncen za a yanke ne bayan an saurari lauyoyin bangarorin.

Harabar kotun da cikin kotun dai sun cika makil da jama' wadanda suke jira su ji hukuncin da za a yanke a lokacin.

Shari'o'in da ake sa ran yi sun hada ne da na Samuel Ortom na jam'iyyar PDP da kuma Emmauel Jime na jam'iyyar APC daga Benue, sai kuma na jihar Filato tsakanin Jeremiah Useni na jam'iyyar PDP da kuma Simon Bako Lalong na jam'iyyar APC.

Akwai kuma shari'a tsakanin Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad na jam'iyyar PDP da kuma Mohammed Abdullahi Abubakar na jam'iyyar APC.

Akwai shari'a tsakanin Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC inda yake kalubalantar Aminu Waziri Tambuwal na PDP, sai kuma a jihar Imo akwai shari'a tsakanin Hope Uzodimma na jam'iyyar APC inda yake kalubalatantar nasarar Emeka Ihedioha a zaben gwamnan jihar.

Labarai masu alaka