Rikici tsakanin Masar da Habasha: Rikici kan Kogin Nilu

Ginin Babbar madatsar ruwan da za a farfado da shi na Habasha kan kogin Nilu. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Babban dam na Grand Renaissance da za a farfado da shi abin alfahari ne ga Habasha

Ana shirin komawa kan tattaunawa kan batun magance matsalar da ke tsakanin Habasha da Masar kan makomar babbar tashar lantarki da ake samarwa ta hanyar ruwa a Kogin Nilu nan gaba kadan a Washington.

A bara dai, an tsayar da 15 ga watan Janairu a matsayin wa'adi domin magance matsalar da ta dade tsakanin kasashen biyu.

Sai dai a makon da ya gabata, an tashi ba tare da cimma matsaya ba.

Idan aka kammala ginin dam din, zai zama tashar lantarki mafi girman makamashin samar da wutar lantarki ta ruwa a Afirka.

An fara ginin ne a shekarar 2011 a kan Kogin Nilu da ya bi ta arewacin Habasha, inda kuma kashi 85% na ruwan yake kwararowa.

Sai dai dam din ya janyo rikici tsakanin Masar da Habasha, da kuma Sudan a tsakani, wanda wasu ke fargabar yana iya kaiwa ga yaki, amma a yanzu Amurka tana kokarin kawo sulhu.

Me yasa ake ganin zai iya kawo rikici?

Ana tsaka da rikicin ne kuma ake shirin cika ruwan kogin, yayin da Masar ke ganin aikin zai bai wa Habasha damar samun karfin iko kan kwararan kogin mafi tsawo a Afirka.

Tashoshin samar da wutar lantarki ta ruwa ba su cika amfani da ruwa ba, sai dai hanzarin da Habasha ke yi wajen cika ruwan kogin na iya shafar kwararar ruwan.

Tsawon lokacin da aka dauka wurin cika ruwan kogin, wanda zai fi na Greater London girma, shi ne zai rage hadarin tasowar ruwan.

Habasha na so ta kammala aikin cikin shekara shida

"Muna da shirin fara cika shi a damina mai kamawa, kuma za mu fara samar da wutar lantarki da injin samar da ruwan guda biyu zuwa Disamban wannan shekarar," inji Ministan ruwa na Habasha Seleshi Bekele a watan Satumban da ya gabata.

Amma Masar na so a ba ta lokaci mai tsawo - ta yadda ruwan kogin ba zai yi kasa ba, musamman a matakin farko na cika ma'adanan ruwa.

Tattaunawa ta hanyoyi uku tsakanin Masar da Sudan da kuma Habasha kan kogin da kuma cika ma'adanar ruwan ba ta cimma gaci ba cikin fiye da shekara hudu da aka shafe - wanda a yanzu Amurka ke kokarinshiga tsakani.

Bayan tattaunawa da a kayi a makon da ya gabata, Mista Seleshi ya zargi Masar da rashin niyyar cimma yarjejeniya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ministan ruwan Habasha ya ce za su fara cike ma'adanar ruwan a watan Yuli

"Ba na jin lokacin da 'yan Habasha suka zo nan sun zo da shirin cimma yarjejeniya", Kamar yadda Mista Seleshi ya Shaida wa BBC.

"Sai kuma suka zo da wani sabon jadawalin cike ma'adanar da suka shirya. Sabon jadawalin ya bukaci a cike ma'adanar cikin shekara 12 zuwa 21.

"Wannan ba gwajin da za a amince da shi ba ne a ko'ina", inji Seleshi.

An ruwaito Ministan ruwa na Masar, Mohamed Abdel Aty, na cewa, bangarorin duka sun fahimci batun, har da batun cike ma'adanar ruwan.

Me ya sa Masar ta harzuka?

Masar ta dogara kan Kogin Nilu da kashi 90% domin samun ruwa.

Akwai hasashen tarihi da ke cewa samun tsayayyen ruwa na Nilu abu ne muhimmi ga rayuwar 'yan kasar da ke fama da karancin ruwa.

Wata yarjejeniyar shekarar 1929 (da kuma wata da aka sake a 1959) ta bai wa Masar da Sudan damar amfani da kusan dukkanin ruwan kogin Nilu.

Wasu takardun bayanai na lokacin mulkin mallaka sun bai wa Masar karfin iko kan duk wani aiki da wata kasa za ta gudanar kan madatsar ruwan matukar zai shafi rabon samun ruwansu.

Babu daya daga cikin yarjejeniyoyin da ta tanadi wani alawus ga mazauna gabar ruwan da ba sa cikin yarjejeniyar, ciki har da Habasha, wadda Kogin Blue Nile dinta ke bayar da babbar gudunmawa ga ruwan Kogin na Nilu.

Habasha ta ce ba za ta yi amfani da yarjejeniyar ta shekara da shekaru ba wajen kafa masu takunkumi.

Sai ta yi gaban kanta ta fara gina tata madatsar ruwan a lokacin guguwar juyin-juya hali ta yankin Gabas ta Tsakiya ta 2011 ba tare da shawartar Masar ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ruwan Kogin Nilu na kwarara ta birnin Aswan da ke Masar, kimanin kilomita 920 daga kudancin babban birnin kasar Alkahira

A watan Satumban shekarar da ta gabata ne aka ruwaito Shugaban Masar Abdul Fattah al-sisi na cewa hakan ba za ta faru ba da a ce guguwar sauyin kasashen Larabawan ba ta dauke hankalin kasarsa ba.

Wani abin da da ke damun Masar shi ne, idan har kwararar ruwan ta ragu hakan zai iya shafar tafkin Nasser, da kuma raguwar ruwan da ke cikin ma'adanar kogunan, a gefen dam din Aswan, wanda daga nan ne Masar ke samun mafi yawan wutar lantarkinta.

Habasha ta ce daya daga cikin sharuddan da Masar ta gidanya mata kan yarjejeniyar shi ne a hade sabon dam din da Aswan.

Mista Seleshi ya shaida wa BBC cewa ya yi wa 'yan kasar Masar bayani cewa "abu ne mai wuya a hada madatsun biyu".

Me ya sa Habasha ke son babbar madatsar ruwa irin wannan?

Madatsar ruwan da za a kashe wa kudi dala biliyan hudu na daga cikin burin da kamfanonin masana'antun Habasha ke so su cimma. Idan aka kammala, ana sa ran za ta samar da kimanin wutar lantarki da mai karfin megawatts 6000.

Habasha na fama da matsanancin karancin wutar lantarki, inda kashi 65% na al'ummarta ba sa samun wutar a-kai-a-kai.

Makamashin da za a samar zai isa al'ummar su samu wuta a kuma sayar da rarar wutar lantarkin ga makwabtakan kasashe.

Haka kuma Habasha na yi wa madatsar ruwan kallon abu na kare martabar kasa.

Aikin madatsar ruwan bai dogara kan kudin daga kasashen waje ba, ya dogara ne kan gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu.

Kasar na kokawa kan batun da take kallo a matsayin katsalandan daga kasashen waje cikin batun.

Ko akwai wani daban da zai amfana?

Kwarai kuwa. Makwabtan kasashe irin su Sudan da Sudan ta Kudu da Kenya da Djibouti da kuma Iritiriya na daga cikin wadanda ake sa ran za su amfana daga wutan lantarkin da madatsar za ta samar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Habasha nafatan za a kammala aikin a shekarar 2020

Yawancin wadannan kasashen na fama da matsalolin karancin wutan lantarki.

Ga kasar Sudan, suna da karin samun dama saboda madatsar ruwan za ta rika lura da yadda ruwan ke kwarara - wannan na nufin ruwan zai kasance iri daya a duk tsawon shekara.

Da ma dai kasar na fama da ambaliyar ruwa sosai a watannin Agusta da kuma Satumba.

Ko rikicin zai iya kai wa ga yaki?

Akwai fargabar kasashen na iya shiga yaki idan har ba su sulhunta ba.

A shekarar 2013, an samu bayanan sirri da aka nada da ke bayyana yadda 'yan siyasar Masar ke kokarin far wa Habasha kan ginin dam din.

An ruwaito cewa shi ma Shugaba Sisi na cewa Masar za ta dauki dukkannin matakan da ya dace domin kare hakkokinsu kan ruwan Nilu.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata, Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya fada wa Majalisar Wakilai cewa babu wani karfin iko da zai dakatar da Habasha daga gina madatsar.

Kungiyar International Crisis Group mai lura da rikici ta yi gargadi a bara cewa kasashen "na iya shiga fagen yaki" kan madatsar ruwan.

Sa bakin da Amurka ta yi kan batun na nuna kamarin al'amarin - da kuma bukatar da ke akwai ta kawo karshen matsalar.

To me zai faru yanzu?

Mataki na gaba shi ne ministocin ruwa tare da ministocin harkokin kasashen waje na kasar suyi kokarin cimma yarjejeniya kafin wa'adin da aka ba su na 15 ga watan Janairun tun a bara.

An sanya wa'adin ne a watan Nuwamban bara bayan ganawa tsakanin kasashen da Sakataren Baitulmali na Amurka Steven Mnunchin da kuma Shugaban Bankin Duniya David Malpass.

Ana sa ran wakilan kasashen za su sake haduwa a Washington nan gaba kadan.

Hakkin mallakar hoto US president's office
Image caption Donald Trump na fatan Amurka za ta iya samar da yarjejeniya tsakanin kawayen nata biyu

Idan har wakilan suka gaza cimma matsaya zuwa 15 ga watan Janairu, masu sulhun za su bukaci wani mai shiga tsakanin daban ko kuma a aika da batun ga shugabanninsu, kamar yadda yarjejeniyar watan Nuwamban bara ta tanada.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC