Taron Faransa: Rikicin yankin Sahel ya zama karfen kafa

Sojoji a yankin Sahel Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akwai dubban dakaru har daga Nijar da suke shawagi a yankin domin yakar 'yan bindiga

Shugaban Faransa da takwarorinsa daga yankin Sahel sun tattauna kan yakin da sojoji ke yi da masu da'awar kishin Musulunci a yammacin Afirka.

Mun duba alkaluman da ke bayan rikicin da ke ci gaba da ta'azzara.

Hare-hare kan sansanin sojoji da fararen hula a sassan yankin na ci gaba da faruwa duk da kasancewar dubban dakaru daga kasashen da abin ya shafa da Faransa.

An samu mace-mace mafi muni a shekarar da ta gabata sakamakon rikici a yankin tun shekarar 2012.

A makon da ya gabata, sojoji 89 daga Nijar aka kashe a wasu hare-haren baya-bayannan da gwamman dakaru suka mutu a yankin.

Faransa ita ma ta rasa sojojinta 13 a wani hadarin jirgi mai saukar ungulu a Mali cikin watan Nuwamba.

Yankin Sahel, da ke kudu da Hamadar Sahara na gaba-gaba a yaki da masu da'awar kishin musulunci kusan shekara 10.

Sai dai matsalar da ke addabar Chadi da Nijar da Mali da Burkina Faso da Mauritania da ake kira G5 Sahel ba ita ce kawai ba kuma akwai bukatar karin dakaru domin magance matsalar da sauyin yanayi da sauran kalubalen ci gaba.

Babban abin damuwar shi ne rikicin na iya bazuwa zuwa wasu sassan yankin Afirka ta yamma.

1. Tabarbarewar rikicin

Matsalar tsaro a yankin ta fara a 2012 lokacin da hadakar kungiyoyi masu da'awar kishin musulunci suka kwace iko da arewacin Mali abin da ya sa Faransa ta kai daukin dakaru domin fatattakar kungiyoyin yayin da suke kara karfi a Bamako babban birnin kasar.

An sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a 2015 sai dai ba a aiwatar da ita ba sannan kungiyoyin ta'adda tuni suka bullo kuma suke yaduwa zuwa tsakiyar Mali da Burkina Faso da kuma Nijar.

Mutanen da suka mutu sanadiyyar hare-haren a kasashen sun karu tun 2016 inda aka rawaito mutane 4,000 sun mutu a shekarar da ta gabata kadai.

2. Wuraren da suka fi hadari

Yankin da ya rufe yankunan kan iyaka da Burkina Faso da Mali da kuma Nijar, shi ne cibiyar ayyukan ta'addanci da ayyukan yaki da ta'addanci.

Kungiyoyi masu rike da makamai, wadanda suka hada da wasu dake da alaka da al-Qaeda da kuma kungiyar masu da'awar kishin musulunci suna kara girma da samun karfi iko.

Dalilan da suka janyo yaduwar su suna da yawa:

  • Rashin tsaro kan iyakoki da karancin jami'an tsaro a wasu yankunan.
  • Sun kafa ayyukan samun kudade kamar kakaba haraji da safarar miyagun kwayoyi da makamai da mutane abin da ke taimaka musu tafiyar da harkokinsu.
  • Da alama sojoji da ke yaki da 'yan ta'adda basu da cikakken horo da rashin makamai duk da tallafin da suke samu daga kasashen duniya.

Baya ga kasashen G5 Sahel da suke da dakaru 5,000 dake yakar masu tada kayar baya, Faransa ta aike sojojinta 4,500 zuwa yankin na Sahel tun 2013.

Majalisar dinkin duniya tana da dakarun kwantar da tarzoma 12,000 a Mali yayin da Amurka ta ke da sansanonin jirage marasa matuka biyu a Nijar inda take samar da bayanan tsaro da horas da sojoji a yankin.

An samu bullowar kungiyoyin da ke kare kansu duk da karuwar matsalar rashin tsaro.

A Mali da Burkina Faso, ana tunanin kungiyoyin ne suka haddasa mutuwar mutane da dama.

3. Ba 'yan tadda ba ne kadai ke haifar da tashin hankalin

Babu masu daukar nauyin mafi yawan hare-hare kan farar hula sai dai kungiyoyin da ke da'awar kishin musulunci a yankin Sahel sun hada da:

  • Al-Qaeda mai alaka da Jama'a Nusrat ul-Islam wa al-Muslimin - JNIM
  • Kungiyar IS a yankin kudu da hamada
  • Ansarul Islam
  • Katiba Macina
  • Bullar sauran kungiyoyin tsaro da ke da alaka da kabilanci ko siyasa.

Ana hada rikice-rikicen kabilanci da takaddamar tattalin arziki da rikicin masu da'awar kishin musulunci inda ake zargin kabilar Fulani Musulmi na da alaka da kungiyar 'yan ta'adda - zargin da Fulanin suka musanta.

Kazalika, fadada hamada da canjin yanayi ya kara haifar da rikice-rikice na dogon lokaci tsakanin Fulani makiyaya da manoma.

Wannan ya haifar da kafuwar kungiyoyin yaki da kabilanci a bangarorin biyu, wadanda suka dauki nauyin mummunan kisan gilla kan mutane.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun zargi wasu dakaru da kashe farar hula ba bisa ka'ida ba a yakin da suke da ta'addanci.

A makon da ya gabata, wata gamayyar kungiyar farar hula ta ce "ayyukan dakaru a yankin Sahel na daga cikin matsalar".

Kungiyar Action Against Hunger mai yaki da yunwa da hukumar kula da 'yan gudun hijra ta Norway da Oxfam sun kiyasta cewa ayyukan dakaru a Mali sun tilastawa sama da mutane 80,000 kauracewa gidajensu - kimanin kashi 40 cikin dari na dukkanin mutanen da suka rasa muhallansu a kasar.

4. Yadda rikicin ya sa mutane kauracewa muhallansu

Yayin da yawan mutanen da ke yankin zai karu nan da shekara 20, tashin hankali a yankin na kara haddasa matsalolin rashin ci gaba.

Samar da abinci ga kowa zai zama kalubale kuma adadin mutanen da aka tilasta musu tserewa daga gidajensu ba ya taimakon lamarin.

A Burkina Faso, adadin mutanen da suka rasa muhallansu ya karu daga 40,000 a karshen 2018 zuwa sama da 500,000 a karshen 2019 - sama da kashi biyu cikin dari na al'ummar kasar. A Mali kuwa, yawan mutanen ya ninku.

Rikicin na kuma janyo matsaloli ga manyan gobe yayin da wasu kungiyoyi masu da'awar kishin musulunci suke kai hare-hare kan makarantu da malamai tare da barin dubban yara rasa damarsu ta ilimi.

Yaran kuma na fuskantar cin zarafi kala-kala kama daga fyade da bautarwa ko sanya su cikin kungiyoyin ta'adda.

Mafi yawan bayanan da ke cikin wannan rahoton an samo su ne daga Armed Conflict Location & Event Data Project (ACLED)

Labarai masu alaka