Buhari ya saka hannu kan dokar kudi ta Finance Bill 2019

Shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidencey
Image caption Buhari ya gabatar da kudirin dokar tare da kasafin kudi a watan Oktoba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya saka hannu kan dokar kudi, wadda za ta samar da hanyoyin aiwatar da kasafin kudin 2020, kamar yadda shugaban ya bayyana.

"Wannan ne karon farko tun bayan dawowar dimokuradiyya a Najeriya a 1999 da aka kaddamar da kasafin kudi tare da dokar aiwatar da shi a Najeriya," in ji Buhari.

Dokar mai suna Finance Bill, 2019, za ta taimaka wa masu manya da matsakaita da kananan san'o'i wurin yin kasuwancinsu cikin sauki.

Sannan kuma ta taimaka wa gwamnati wurin samun isassun kudi da kuma taimakawa wurin karfafa gwiwar masu zuba jari.

Buhari ya gode wa shugabannin majalisun tarayya, wadanda a cewarsa "suka yi aiki tukuru domin tabbatar da kudirin dokar wadda ke da matukar amfani wurin aiwatar da kasafin kudin 2020".

Idan za a iya tunawa dai, shugaban ya gabatar da kudirin dokar ne yayin da yake gabatar da kasafin kudin 2020 a zaman hadin gwiwar Majalisun Tarayya a watan Oktoba.

Buhari ya fada a lokacin cewa kasafin kudin kacokam ya dogara ne kan tanadin dokar, wadda ta sahhale kara kudin harajin kayayyaki daga kashi 5% zuwa 7.5%.

Aikin da dokar za ta yi

  • Yi wa dokokin karbar haraji garambawul
  • Tallafa wa kanana da matsakaitan 'yan kasuwa
  • Karfafa wa masu zuba jari gwiwa a manyan ayyukan raya kasa
  • Tara wa gwamnati karin kudin shiga

Labarai masu alaka