Sarauniya ta amince da matakin Harry da Meghan

The Duke and Duchess of Sussex Hakkin mallakar hoto Getty Images

Sarauniya ta amince da "sauyin" da Yarima da matarsa Gimbiyar Sussex suka zo da shi na tafiya Canada da kuma Birtaniya don samun lokaci.

Ta ce ta ba su goyon baya dari bisa dari kan burinsu na gudanar da sabuwar rayuwarsu "amma dai za ta fi son" su kasance cikakkun masu sarauta.

Ta ce tana sa ran yanke shawarar karshe a kwanaki kadan masu zuwa.

Manyan 'yan gidan sarautar Birtaniya na ta tattaunawa kan bukatar Harry da Meghan bayan da suka ce suna so su ajiye mukamansu na sarauta.

A wata sanarwa, saraunuyar ta ce tattaunawar da ake yi a Sandringham, wadda ta hada da Yariman Wales da kuma Yariman Cambridge ta kasance "mai muhimmanci".

"Ni da ilahirin iyalina mun bai wa Harry da Meghan cikakken goyon baya kan burinsu na fara sabuwar rayuwa a matsayinsu na iyali masu tasowa".

'Karin rayuwar zaman kansu'

"Duk da cewa mun fi so su kasanace cikakkun 'yan gidan sarauta, amma mun girmama zabinsu na zaman kansu yayin da za su ci gaba da kasancewa wani muhimmin bangare na iyalina."

"Wannan lamari mai sarkakiya ne ga iyalina kuma har yanzu akwai sauran aiki amma na bukaci a yanke hukuncin karshe a 'yan kwanaki masu zuwa," in ji Sarauniya.

An yi wannan tattaunawar ne bayan yariman da matarsa suka bai wa gidan sararutar mamaki a ranar Laraba da cewa za su fara "rayuwar zaman kansu" sannan za su ci gaba da rayuwa ne tsakanin Birtaniya da kuma arewacin Amurka.

Ta ya ya abin ya kawo haka?

A wani sako da suka wallafa a shafinsu na Instagram, yariman da matarsa sun ce za su "ja baya" daga matsayin manyan 'yan gidan sarautar Birtaniya sannan su koma arewacin Amurka "yayin da za mu ci gaba da yi wa Sarauniya hidima da kungiyar Commonwealth da sauran alkawura".

Wannan ya zo ne bayan wata hira ta musamman da suka yi a watan Oktoba, inda suka bayyana rashin jin dadinsu kan yadda kafafen yada labarai ke bayyana su.

Kazalika, ma'auratan suna shirin kafa wata gidauniyar gidan sarauta tasu ta kansu, wadda suka kafa bayan sun fice daga ta masarautar a watan Yuni.

Jadawalin masu sarautar Birtaniya

Labarai masu alaka