Wani ya yi kokarin fataucin buhun kunama a Sri Lanka

A type of scorpion Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mahukunta sun yi imanin cewa an yi fataucin kunamar ne saboda amfani da dafinta Authorities

An kama wani dan China da ya yi kokarin fataucin kunama daga Sri Lanka.

Jami'an tsaron Colombo ne suka kama kunamar a cikin wata jika.

Mahukunta na tunanin mutumin ya shirya fita da kunamar ne domin cire dafinta idan ya isa China.

Yaki da fataucin namun daji da zinari da kuma muggan kwayoyi wani babban kalubale ne a Sri Lanka.

An ci tarar mutumin kudi dala $550 inda kuma aka amince ya koma kasarsa.

Sri Lanka na da nau'in kunamu, kuma daya daga cikinsu ce kawai ke barazana ga mutane. Babu dai tabbaci ko fataucin kunamar wani hatsari ne.

Sri Lanka dai ta tsaurara dokoki kan fataucin dabbobi musamman na dawa, yayin da matsalar ke ci gaba da karuwa.

A watan Yuni an kama wasu jami'an kasar da suka yi kokarin fataucin jinjirar giwa.

Shekarun baya, Sri Lanka ta kama jemagu da aka kama, wadanda mafi yawanci mutanen China da wasu kasashen Asiya ke amfani da su a abinci.

Labarai masu alaka