Shari'ar gwamnoni: An tsaurara tsaro a Kotun Koli

Kotun koli

Yayin da ake dakon yanke hukunci kan shari'ar zaben wasu gwamnoni a kotun koli ta Najeriya, a yau Talata an jibge dimbin jami'an tsaro a kan hanyoyin dake kai wa kotun da ma harabar kotun.

Wakilin BBC Sani Aliyu da ya isa harabar kotun tun da sanyin safiya, ya ce sai da ya shafe kimanin minti 30 yana bin matakai daban-daban na jami'an tsaro gabanin kai wa harabar kotun.

To sai dai duk da haka tuni kotun ta yi cikar kwari da lauyoyi da kuma magoya bayan wasu 'yan siyasar da za a yanke hukunci kan shari'ar ta su.

A ranar Litinin ne dai kotun to koli ta dage zamanta zuwa Talata bayan ta fara sauraron kara ta farko, saboda abin da ta bayyana rashin lafiyar daya daga alkalai bakawai da za su yanke hukunce-hukuncen.

Sai dai wasu na ganin irin cikar da kotun ta yi da kuma yadda jami'an tsaro suka gaza fitar da mutane daga zauren kotun na daga dalilan da suka sa aka dage zaman kotun.

A yau din dai ana sa ran yanke hukunci ne kan shari'ar zaben gwamna na jihohin Kano da Bauchi da Sokoto da Filatoda Imo da kuma Benue.

Tuni dai aka fara sauraron kara ta farko, wato shari'a tsakanin Abba Kabir Yusuf na PDP Kano da hukumar zabe da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na APC a bangare daya.