An sace dagacin Karshi a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano

'yan sanda Hakkin mallakar hoto Nigeria Police

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da sace dagacin Karshi a karamar hukumar Rogo.

An sace hakimin ne ranar Litinin a kauyensa da ke yankin kudancin Kano.

Garin nasa na iyaka da jihar Kaduna.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Kano ta ce ta tura wata runduna ta musamman domin neman dagacin da kuma kubutar da shi.

Ana kara samun yawaitar sace mutane domin kudin fansa a wasu jihohin Najeriya, tun bayan da abin ya yi kamari a shekarar 2019.

A watan Mayun 2019 ma an sace Magajin Garin Daura bayan da wasu 'yan bindiga sun kai hari garin Daura a jihar Katsina - wato mahaifar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Kazalika a watan Nuwambar 2019 ma wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun yi awon gaba da Sarkin garin Rubochi da ke karkashin karamar hukumar Kuje ta Abuja.

Za mu kawo muku karin bayani nan gaba kadan.

Labarai masu alaka