Mutum 30 sun mutu a hatsarin mota a Ghana

hatsarin ghana Hakkin mallakar hoto Star FM Ghana
Image caption Motocin sun yi arangama da juna a kan babban titin nan da ya yi kaurin suna na Capecoast da Takoradi

Rundunar 'yan sandan Ghana reshen yankin gabas ya tabbatar da mutuwar sama da mutum 30 yayin da wasu da yawa suke can asibiti rai a hannun Allah, sakamakon hadarin mota a kan babban titin Capecoast-Takoradi da ke jihar tsakiya.

Kazalika rundunar ta kuma ce ana neman wasu mutum 17 da ba a ga gawarsu ba a hatsarin.

Rahotanni sun ce hadarin ya faru ne da tsakar daren Litinin bayan wasu motocin safa-safa guda biyu sun yi taho mu gama.

Motocin sun yi arangama da juna ne a kan babban titin nan da ya yi kaurin suna na Capecoast da Takoradi.

Wasu daga cikin mutanen da hadarin ya rutsa da su an garzaya da su ne zuwa asibitin koyarawa na Takoradi, wasu kuma an kai su wani asibiti da ke Capecoast.

Kawo yanzu dai adadin mutanen da aka tabbatar da mutuwarsu a asibitin Capecoast sun fi 30, sai dai har yanzu ba a samu wani adadi ba daga asibitin Takoradi.

Da yawa suna cikin mumnanan yanayi,yayin da ake neman wasu fasinjojin kusan goma 17.

Hanyar dai ta yi kaurin suna wurin abkuwar hadarruka saboda dalilai da yawa.

Sai dai wani fasinja da ya tsallake rijiya da baya ya dora laifin ne a kan rashin fitilun kan titi da kuma direban daya motar.

"Ni da kaina direba ne amma bai kamata direba ya yi kokarin wuce wata mota da ke gabansa ba a kan kwana.

"Don haka laifin daya direban ne, direbanmu ya yi iya kokarinsa don ya kauce amma ina, aikin gama ya gama," a cewar fasinjan.

Labarai masu alaka