Dalilin da yawan hayayyafa ya zama matsala a Rasha

Russian child plays in park with his mother in Moscow (9 January) Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban Rasha ya yi magana ne a lokacin da ake fuskantar barazanar raguwar al'ummar kasar

Shugaban Rasha, Vladmir Putin ya gabatar da tsarin inganta walwala da nufin habaka yawan haihuwa bayan da wani hasashe da aka yi ya nuna za a samu raguwa a al'ummar kasar.

A jawabinsa na shekara-shekara ga majalisar dokokin kasar, Putin ya ce makomar Rasha ta dogara ne kan yawan al'ummar kasar.

Mista Putin ya ce ya zama wajibi kasar ta tallafa wa matasa da ke da burin yin aure.

Ya kuma gabatar da kuri'ar raba gardama kan sauya kundin tsarin mulkin kasar domin bai wa 'yan majalisar dama wajen zabar Firai Minista.

Putin ya rike mukamin na Firai Minista na tsawon shekara hudu lokacin da doka ta haramta masa zama shugaban kasa.

Dalilin da ya sa yawan hayayyafa ya zama matsala a Rasha

Akasarin kasashen gabashin Turai na fama da matsalar raguwar yaran da ake haifa.

Ko a makon da ya gabata, Firai Minista mai tsatsatsauran ra'ayin siyasa a Hungary, Viktor Orban ya sanar da kudirin rarraba maganin haihuwa ga ma'aurata da kuma dauke biyan haraji ga iyaye mata masu 'ya'ya uku ko sama da haka.

Tuni aka bai wa iyaye mata masu yara hudu hutun biyan haraji a Rasha, kasar da ke da kashi 1.48 na yawan haihuwa.

Yawan al'ummar Rasha na fuskantar kalubale wajen farfadowa da ga raguwar da ya yi a shekarun 1990 har ta kai ga Mr Putin ya ce a shekarar 1999, hayayyafar da ake yi ta ragu zuwa 1.16, kasa da yadda take a lokacin yakin duniya na biyu.

Amma hayayyafar ta karu a shekarun baya-bayan nan, duk da cewa dai yawan al'ummar kasra a yanzu miliyan 147 ne.

Shin hakan zai yiwu?

An fara bayar da bashin jarirai na kashi daya ne a cikin Rusha a 2007 a wani bangare na shirin shekaru 10 kuma ya yi nasarar kara yawan iyalai da yara biyu, in ji masaniyar ilimin shaye-shaye, Farfesa Evgeny Yakovlev.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba wai kawai a Rasha ba ne ake fuskantar raguwa a hayayyafar da ake yi a 'yan shekarun nan

Ya shaida wa BBC cewa "Sai dai tun 2017, hayayyafar ta sake raguwa. Iyalai sun daina haihuwa. Suna tsoron rashin tabbas game da kudi,"

Kudin da ake biya a yanzu ya kai kimanin dala 7,600 sai dai wani kwararre a Rashan Anatoly Vishnevsky yana ganin fadada tsarin zuwa sauran iyalai ba zai yi wani tasiri ba saboda tsarin raguwar hayayyafar iri daya ne da sauran kasashen da suka ci gaba.

Me Putin ya kara cewa?

Wannan shi ne jawabin shekara-shekara karo na 16 da Mr Putin ya ke ga majalisar dokokin kasar da ake kira Duma kuma Mr Putin ya yi amfani da jawabin nasa wajen yin magana kan makomarsa anan gaba.

Wa'adin mulkinsa na hudu zai zo karshe a 2024 kuma a tsarin dokar kasar, zai sauka daga mukaminsa ne idan lokacin ya cika.

Yayin da ya ke cewa yana son ya ci gaba da tafiyar da tsarin shugabancin kasar a tsarin da yake, Mr Putin ya gabatar da kuri'ar raba gardama kan sauya kundin tsarin mulkin kasar domin bai wa 'yan majalisar ikon nada firai minista.

A tsakanin wa'adin mulkinsa na biyu da na uku, Mr Putin ya zama firai minista kafin komawa kan kujerar shugaban kasa a 2012 kuma a ka'ida yana iya sake zama firai minista.

Ko lokacin da ya ke firai minista, ana kallon Mr Putin amatsayin mai fada a ji a gwamnatin Shugaba Dimitry Medvedev a lokacin.

Labarai masu alaka