Hope Uzodinma: Abubuwan da ba ku sani ba game da sabon gwamnan Imo

Govnor Hope Uzodinma

An rantsar da Sanata Hope Uzodinma a matsayin sabon gwamnan jihar Imo a kudu maso gabashin Najeriya a wani biki da aka gudanar a dandalin Heroes Square.

Kafin rantsar da shi, sai da hukumar zabe ta kasar, INEC ta mika masa takardar shaidar lashe zabe a ofishin hukumar da ke Abuja, babban birnin kasar.

Shugabar sashen shari'a a INEC, May Agbamuche ta ce sun ba shi takardar lashe zaben bayan da kotun kolin kasar ta yanke hukunci kan hakan.

Hope Uzodinma ya gode wa jami'an hukumar INEC bisa bin umarnin kotu inda ya ce nasarar da ya samu a kotu ta nuna cewa kotu ce gatan talaka.

Ya bayyana cewa yana da burin yi wa al'ummar Imo aiki da kuma tabbatar da shugabanci nagari.

A ranar Talata ne kotun kolin kasar ta sanar da korar Honourable Emeka Ihedioha daga kan kujerar gwamnan Imo, tare da ayyana Sanata Hope Uzodinma a matsayin sabon gwamna kuma wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a 2019.

Hukuncin kotun dai ya zo wa 'yan Najeriya da ba-zata.

Bayan yunkurinsa na zama gwamnan Imo sau biyu, na farko a 2003 karkashin jam'iyyar ADP da kuma 2006 karkashin inuwar PDP, a yanzu Uzodinma wanda yake jam'iyyar APC ya samu cikar burinsa.

Wanene Hope Uzodinma, me muka sani game da shi?

An haifi Sanata Hope Uzodinma a 1959.

Ya yi makarantar sakandaren Mgbidi da ke Oru ta yamma a shekarar 1982 sannan ya samu digirinsa na farko a ilimin huldar dimokradiyya sannan ya samu babbar diploma a ilimin sufuri.

Iyali

Gwamna Hope Uzodinma yana da aure da kuma 'ya'ya shida.

A shekarar 2015 ya auri matarsa ta biyu, Chioma Ikeake sai dai ba a yi gagarumin biki ba sannan kuma suna da yaro daya.

Matarsa ta farko Augusta Uzodinma mai yara biyar ta taba magana kan yunkurin da mijin nata yake na kara aure a majami'ar Katolika.

Sai dai Sanatan ya ce cocin katolikan da kuma kotu sun raba auren shekara 17 da suka gabata.

Zaben gwamna na 2019

Sanata Uzodinma ya fice daga PDP inda ya koma APC a 2018 domin samun damar tsawaya takarar gwamna.

Ya shiga zaben fitar da gwani har sau biyu kuma ya samu nasara.

Na farko shi ne zaben fitar da gwanin da aka yi a Abuja inda AhmedGulak, Shugaban kwamitin zaben fitar da gwani na APC ya sanar da shi a matsayin wanda ya yi nasara.

Zaben fitar da gwani na biyun kuma shi ne bayan da tsohon gwamna, Rochas Okorocha ya yi watsi da tsaida shi da jam'iyyar ta yi inda ya bukaci a sake sabon zaben fidda gwanin.

Hakkin mallakar hoto Facebook

Sanata a Tarayyar Najeriya

Hope Uzodinma ya zama sanata mai wakiltar Imo ta yamma a babban zaben kasar da aka yi a 2011 karkashin jam'iyyar PDP.

Sai dai an kalubalanci nasarar da ya yi a zaben tare da zargin cewa ba shi ne halastaccen dan takarar PDP ba amma kuma kotun koli ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Zargin cin hanci

Kamar akasarin 'yan siyasar Najeriya, ana tuhumar Uzodinma da cin hanci da rashawa.

A karar da mai shari'a Chukwudifu Oputa ya saurara a 2001, an zargi Uzodinma da kokarin tura wasu makudan kudade daga hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta kasar zuwa tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Abdussalami Abubakar.

Kazalika a 2005, Dere Awosika, makusanciya ga mai dakin shugaban kasa a lokacin, Stella Obasanjo ta zarge shi da badakala wajen bada kwangila.

Ta ce kamfaninsa da na Awosika suna samun naira miliyan 250 sai Uzodinma ya mayar da nasa kudin bayan hukumar da ke yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati, EFCC ta matsa masa lamba.

A 2009 kuma, EFCC ta tsare shi bisa ikirarin da ta yi cewa bankin Spring ya mika mata kokensa a 2005 cewa Uzodinma na son karbar kudade ta haramtacciyar hanya kuma har yanzu batun yana gaban EFCC.