Kare "ya kashe jariri sabuwar haihuwa" a Indiya

Baby feet Hakkin mallakar hoto Ankit Srinivas

'Yan sanda a India na binciken zargin da wasu iyaye suka yi cewa wani kare ya karci jaririnsu sabuwar haihuwa.

To sai dai asibitin ya dage cewa, ba a haifi jaririn da rai ba.

Jami'ain asibitin sun shiada wa BBC cewa an rufe asibitin da ke arewacin jihar Uttar Pradesh, saboda dama asibitin na gudanarwa ne ba tare da lasisi ba.

'Yan sanda sun ce suna jiran sakamakon gwajin da aka yi domin sanin dalilin mutuwar jaririn.

"Shaidar da aka samu a farko na nuna cewar kare ne ya karce jaririn. Muna binciken yadda aka yi kare ya shiga asibiti," Alkalin yankin Manvendra Singh ya shaida wa BBC.

"Asibitin ya ce ba a haifi jaririn da rai ba kuma jaririn bai mutu saboda harin karen. Amma iyayen jaririn sun ce asibitin na fadin karya ne. Muna gudanar da bincike yadda ya kamata", inji shi.

Mahaifin jaririn ya shaida wa jaridar "Times of India" cewa jaririn na cikin dakin tiyata lokacin da daya daga cikin ma'aikatan ya fito da gudu daga dakin yana cewa, kare ya shigo.

Hakkin mallakar hoto Deepak Kumar Srivastava

"Jaririn nada shaidar karcewar karen a kirjinsa da idonsa na hagu. Yana kwance ya yi shiru", inji mahaifinsa, Ravi Kumar.

Ya kuma zargi ma'aikatan da kokarin ba shi cin hanci domin yayi shiru da maganar yayin da ya tuhume su.

A shekarun baya-bayan nan, Uttar Pradesh ya kasance cikin labarai kan hare-haren kisa da karnuka ke kai wa.

Ko a shekarar da ta gabata ma sai da karnuka suka karce wani jariri dan wata uku da kuma dan shekara bakwai al'amarin da ya yi sanadiyar rasa rayukansu.

A 2018, 'yan kauyen yankin Sitapur sun bayyana cewa karnuka sun kashe yara 12 a hare-haren da su ka kai.

Labarai masu alaka