'Yan sanda na neman matar Firai Ministan Lesotho ruwa a jallo

'Yan sanda na neman matar Firai Minista Thabane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba a san inda Uwar gidan Firai Minista Thabane take ba

'Yan sanda a kasar Lesotho na neman Maesaiah Thabane, matar Firai Minista domin yi mata tambayoyi kan kisar wata matarsa da ba sa tare tsawon shekara biyu da suka wuce.

An yi mamakin yadda Ms Thabane ta bace bat, tun ranar Juma'ar bayan kotu ta ba da sammacinta bayan da ta ki zuwa kotun domin amsa tambayoyi.

An ba ta zuwa yammacin ranar Litinin ta mika kanta ga 'yan sanda.

'Yan sandan masu dauke da makamai sun je neman ta a gidansu na gwamnatin Firai Minista Thomas Thabane ranar Juma'a, sai dai ba su same ta a can ba.

Mai magana da yawun gwamnati Nthakeng Selinyane ya shaida wa shirin BBC Focus on Africa cewa 'yan sandan a shirye suke da su nemi taimakon kasashen duniya wajen neman ta.

An harbe Lipolelo Thabane ne yayin da take kan hanyar zuwa garinsu da kawarta, kwanaki biyu gabanin rantsar da mijinta a watan Yunin shekarar 2017.

Ita da Mista Thabane sun dade ba sa tare tun shekarar 2012.

Shugaban 'yan sanda Holomo Molibeli ya zargi wasu takaddun kotu cewa an kira wata lambar Firai Ministan daga bangaren wadanda ake zargi da kisar, suna alakanta shi da kisar.

Labarai masu alaka