Gwamnatin Najeriya ta haramta kungiyar tsaro ta Amotekun

An samar da motoci da bindigogin gargajiya ga jami'an kungiyar ta Amotekun da zummar yaki da matsalar tsaro a kudu maso yammacin Najeriya Hakkin mallakar hoto The Guardian
Image caption An samar da motoci da bindigogin gargajiya ga jami'an kungiyar ta Amotekun da zummar yaki da matsalar tsaro a kudu maso yammacin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta sanar da haramta kungiyar tsaro ta Amotekun, da wasu jihohin shiyyar kudu suka samar.

Kafa rundunr tsaron ya janyo ce-ce-ku-ce inda wasu ke ganin za ta iya zama barazana ga kasar a nan gaba.

Mai taimaka wa Ministan Shari'ar kasar a fannin yada labarai Dakta Umar Jibrilu Gwandu ya shaida wa BBC cewa batun samar da tsaro da makami hakki ne da ya rataya kan gwamnatin Tarayya.

"Don haka wani bangaren kasar ko ma jihohi ba su da damar kirkirar nasu hukumomin tsaron kamar yadda yake kunshe kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima," in ji shi.

Ya jaddada cewa kirkirar kungiyar wani laifi ne da ya sabawa doka, domin an yi tanadin jami'an tsaron soji da na 'yan sanda da na ruwa da kuma sojin sama, wadanda su ne ke da alhakin tabbatar da tsaro a dukkanin sassan Najeriya.

Ya ce jihohin sun yi gaban kansu ne ba tare da sun tuntubi ofishin ministan shari'a ba kafin daukar matakin kafa rundunar tsaron.

Kafin wannan sanarwa wasu 'yan kasar da dama sun goyi bayan bijiro da kungiyar da suke ganin za ta taimaka wajen yaki da matsalolin tsaro a shiyyar yammaci, ciki har da irin su sanannen marubucin nan Farfesa Wole Soyinka.

Sai dai wasu kuma na bayyana fargaba kan yadda 'yan siyasa za su iya amfani da kungiyar tsaron mai dauke makami domin cimma wasu bukatunsu na siyasa.

Labarai masu alaka