Kalli hotunan tarihi kan yakin basasa na Biafra a Najeriya

A Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Leftenant Kanar Odumegwu Ojukwu, mutumin da ya jagoranci yakin Biafra a lokacin da yake sanar da sabon kudi da a hukumance aka samar ranar 29 ga watan Janairu a wani taron tuntuba a Owerri.

A ranar 15 ga watan Janairun 2020 ne aka cika shekara 50 dakawo karshen yakin basasar da aka yi a Najeriya.

Mutuwar sama da mutum miliyan daya a Najeriya dalilin mummunan yakin basasar da aka yi shekara 50 da ta gabata, ta zama kamar wani tabo ne a tarihin Najeriya.

A shekarar 1967, bayan juyin mulki guda biyu da tashin hankalin da ya janyo 'yan kabilar Ibo kusan miliyan daya komawa yankin kudu maso gabashin kasar, soja Emeka Odumegwu Ojukwu mai shekara 33, ya jagoranci ballewar yankin Biafra.

Mun zabo muku wasu tsofaffin hotuna don tuna baya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dakarun Biafra na kokarin dakile harin sojojin gwamnati a yankin da ke kudu maso gabashin Najeriya, inda yakin basasa don neman 'yancin kai kuma dakarun gwamnati sun kashe kimanin mutane miliyan daya zuwa biyu daga 1967 da 1970.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dakarun gwamnatin Najeriya na shiga Fatakwal bayan samun galaba kan dakarun Biafra lokacin yakin basasa.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani soja ya rike bindigogi lokacin yakin Biafra ranar 11 ga watan Yunin 1968.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu sojoji sun ciccibi wani soja da ya ji rauni a yakin Biafra.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani malamin addini yana yi wa wani dan Biafra addu'a a lokacin yakin basasa a Biafra a 1969.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu 'yan Najeriya sanye da kayan sarki kuma rike da bindigogi a lokacin yakin Biafra. Al'ummar Igbo sun yi tawaye a 1967 inda suke neman kafa jamhuriyar Biafra. Yakin da yunwar da ta biyo baya ya zo karshe ne a 1970 lokacin da sojojin Biafra suka mika wuya ga dakarun gwamnati.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani mutumin Biafra na atisaye da bindiga don tunkarar makiya a filin daga da ke Biafra. An yi yakin basasar Najeriya tsakanin 6 ga watan Yulin 1967 zuwa 15 ga Janairun 1970.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu 'yan Najeriya yayin da suke murna a kan titunan Legas ranar 12 ga watan Janairu sakamakon sanar da kawo karshen yakin Biafra. Gwamnatin Najeriya ta yi na'am da mika wuyan da al'ummar Biafra suka yi tare da yi musu afuwa.

Labarai masu alaka