Russia: Majalisar zartarwar Rasha ta yi murabus

A Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mr Putin ya gana da firai minista ranar Laraba gabanin matakin cewa 'yan majalisar zartaswa za su yi murabus

Majalisar zartarwar gwamnatin Rasha ta yi murabus sa'o'i bayan Shugaba Vladimir Putin ya gabatar da sauye-sauyen kundin tsarin mulkin kasar da zai iya tsawaita wa'adin mulkinsa.

Firai Minista Dimitry Medvedev ya ce shawarwarin da shugaban ya gabatar za su kawo gagarumin sauyi a Rasha.

Mista Putin ya bukaci Medvedev ya zama mataimakin shugaban majalisar tsaron kasar da Mista Putin yake jagoranta.

Sanarwar ba-zatar na zuwa ne shekara hudu kafin wa'adin Mr Putin na hudu a kan karaga ya zo karshe.

Bisa tsarin dokar kasar, Putin na da damar sake neman karin wa'adi kuma shugaban, yayin jawabin da ya yi wa majalisar dokokin kasar, ya ce za a gudanar da zabe a fadin kasar kan sauye-sauyen da zai kara wa majalisar kasar karfin iko.

Wasu majiyoyi daga gwamnatin Rasha sun fada wa BBC cewa ministocin kasar ba su da masaniyar cewa majalisar zartarwar gwamnatin za ta yi murabus gabanin sanarwar.

Daya daga cikin majiyoyin ta ce "abin ya zo da mamaki".

Mista Medvedev ya kasance firai minista na tsawon shekaru.

Ya zama shugaban kasa daga shekarar 2008 zuwa 2012, inda wani makusancinsa ya karbi ragamar shugabancin kasar - bayan da Putin din ya cika wa'adin mulkinsa na daya da na biyu a matsayin shugaban kasa.

Kundin tsarin mulkin Rasha ya bai wa shugaban kasa damar yin zango biyu yana mulkar kasar.

Labarai masu alaka