Wasu daga cikin fina-finai da za su fito a farkon shekarar 2020

Mun zabo maku wasu daga cikin fina-finan Kannywood da za a fitar a farkon shekarar 2020.

LIKITA

Kamfanin Aji Papa ne ya shirya fim din kuma Ibrahim Bala ne ya bayar da umarni. Manyan taurarin wannan fim sun hada da Sadiq Sani Sadiq da Hafsat Idris

KARAMIN SANI

Falalu A Dorayi daraktan fim din. Taurarin fim din sun hada da Adam Zango da Jamila Nagudu da Hadiza Muhammad da sauran su.

Hakkin mallakar hoto Instagram/@falalu_a_dorayi

KAR KI MANTA DA NI

Ali Nuhu ne daraktan fim din kuma manyan taurarin sun hada da Umar M Shareef da Maryam Booth.

Hakkin mallakar hoto Instagram/@realalinuhu
Image caption Kar Ki Manta da Ni

HADIZA MAKAUNIYA

Ibrahim Bala ne ya bayar da umarni. 'Yan wasa sun hada da Sadiq Sani Sadiq da Hadizan Saima da Azumi Bebeji.

Hakkin mallakar hoto Instagram/@famly_investment_limited

KARSHEN TIKA TIKI

Kamfanin Halima Atete ne ya shirya fim din kuma tana cikin jaruman ita da Ali Nuhu.

Hakkin mallakar hoto InSTAGRAM

MATI A ZAZZAU

Kamfanin Sadau Pictures Production ne ya hada wannan fim din. Fitaccen jarumin nan Sadiq Sani Sadiq da kuma mawakiyar nan Dija na cikin wadanda suka fito a cikin sa.

Hakkin mallakar hoto Instagram/@rahamasadau

Labarai masu alaka