'An fi kashe musulmi a hare-haren masu ikirarin jihadi'

Tutar Masu ikirarin Jihadi Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani rahoton da cibiyar Tony Blair Foundation ta fitar ya ce kungiyoyin da ke da'awar jihadi sun fi kashe musulmi fiye da mabiya wani addini a duniya.

Rahoton cibiyar da ta ce ta yi bincike da sa ido kan ayyukan ta'ddanci tun a 2017 a duniya, ya ce kashi 70 na wadanda aka kashe musulmi ne wadanda ba su ji ba su gani ba.

Amma 'yan Shi'a ne rahoton ya ce aka fi kashewa, kuma baya ga musulmai, mabiya addinin Kirista ne aka fi kashewa.

Rahoton kuma ya sanya kasashen Afirka shida a jerin kasashe goma da suka fi fuskantar hare-hare mafi muni na kungiyoyi masu da'awar jihadi.

Najeiya ce ta uku a jerin kasashen da aka fi kashe mutane a duniya bayan Syria da Somalia. Sauran kasashen Afirka sun hada da Mali da Kamaru da Nijar da Masar.

Rahoton ya bayyana yawan kungiyoyi 97 masu da'awar jihadi da ke kai hare-hare a kasashe 46.

Kungiyar Boko Haram da ta addabi kasashen yankin Sahel, rahoton ya ce ta kai hare-hare a Najeriya 226, sannan ta hare hare 187 a kasashen Kamaru da Chadi 187, tare da sace mutum 370.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Boko Haram na ci gaba da zama barazana a Najeriya

Rahoton ya ce duk da ana ikirarin murkushe kungiyoyi, kamar ISIS a Iraqi da Syria, da kuma Boko Haram a Najeriya, amma hakan ba yana nuna an kawo karshensu ba.

A shekaru biyu da suka gabata rahoton ya ce sama da mutum 120,000 aka kashe a hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi, kuma kasashe 68 al'amarin ya shafa da suka hada da manyan kasashen Turai, Birtaniya da Faransa da kuma Jamus.

Barista Abdu Bulama Bukarti, mai nazari kan kungiyoyin ta'addanci a Afrika a cibiyar ta Tony Blair ya shaida wa BBC cewa "girman matsalar ta fi yawa a kasashen Afirka."

"Ya kamata gwamnatocin kashsen Afirka su fahimci wannan matsalar da ta shafe su, sannan su hada kai domin kawo karshenta," in ji shi.

Rahoton ya ce ayyukan masu ikirarin jihadi na ci gaba da zama babbar barazana a duniya.

Labarai masu alaka