Makomar Barkley, Eriksen, Cavani, Kurzawa, Dakonam da Andre Villas-Boas

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Arsenal na son ware fam miliyan £6 domin karbo dan wasan baya na PSG Layvin Kurzawa, mai shekara 27. (Sun)

Arsenal da Tottenham na cikin manyan kungiyoyin Premier biyar da ke son dan wasan Togo na Getafe Djene Dakonam, mai shekara 28, wanda tuni aka yi watsi da tayin Monaco. (Sun)

West Ham ta son karbo aron dan wasan tsakiya na Chelsea Ross Barkley, mai shekara 26, wanda ya yi aiki tare da kocin kungiyar David Moyes lokacin da yana Everton. (Mirror)

Tottenham na tattaunawa kan dan wasan gaba na Cape Verde Ze Luis, mai shekara 28, inda take son karbo aronsa daga Porto. (Record - in Portuguese)

Inter Milan ta amince da yarjejeniya tsakaninta da dan wasan tsakiya Christian Eriksen, mai shekara 27, amma Tottenham na son Inter ta kara kudin da ta taya dan wasan. (Calciomercato - in Italian)

Dan wasan Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 32, da kwangilarsa za ta kawo karshe, kungiyarsa Paris St-Germain ta shaida wa Atletico Madrid ta kara kudi daga yuro miliyan 10 zuwa 30m idan tana son dan wasan. (Marca - in Spanish)

Barcelona na dab da sayen matashin dan wasan Brazil Matheus Fernandes, mai shekara 21, daga Palmeiras kan yuro miliyan 7. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Barca kuma na kokarin karbo matashin dan wasan tsakiya na Japan mai shekara 17 Jun Nishikawa, wanda yanzu haka ke taka leda a Cerezo Osaka. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Tottenham na hamayya da Sevilla kan dan wasan AC Milan Krzysztof Piatek, 24. (Mail)

Labarai masu alaka