Tsoffin Sojin Najeriya sun ce 'an kasa biyansu hakkinsu'
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tsoffin Sojin Najeriya sun ce 'an kasa biyansu hakkinsu'

Latsa alamar lasifika domin sauraren koken tsoffin sojojin na Najeriya:

Wasu tsoffin sojojin Najeriya da suka yi yaki sun koka game da kin biyansu hakkokinsu da gwamnatin kasar ta yi tsawon shekara guda kenan.

Wannan na zuwa yayin da ake cika shekaru 50 da kammala yakin basasar Najeriya sakamakon yunkurin ballewa da yankin gabashin kasar ya yi don kafa kasar Biafra.

Shugaban kungiyar 'yan mazan jiyan Warrant Officer Anthony Agbese  mai ritaya, ya ce tsawon shekara guda kenan suna ta fadi tashin ganin gwamnati ta biya su hakkokinsu amma abin ya gagara.

"Yawancinmu tsofaffi ne, rayuwar mu ta dogara ne akan magunguna, da kudin nan muke amfani muke sayen magani, so ake a yi ta aje mana har sai mun mutu sannan a bamu ne?, in ji shi.

Ya kara da cewa suna kyautata zaton cewa shugaba Muhammadu Buhari bai san da wanan matsala ba, domin yawancinsu tare da shi suka yi yakin Biafra, kuma matsayinsa na soja da yas an ba a bi umarninsa ba da tuni ya dauki mataki.

Sai dai a baya dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya taba bada umarnin tantance sojojin da aka yi yakin da su don biyansu hakkokinsu.

Wasu a kasar na zargin cewa ana tafka mummunan cin hanci a bangaren fansho na kasar, abin da ke kawo matsala a biyan 'yan fanshon da suka shafe fiye da shekaru talatin suna yi wa kasarsu hidima.

Labarai masu alaka