Gwamnatin jihar Katsina ta haramta hawa babur

Acaba Hakkin mallakar hoto Getty Images

Gwamnatin jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta kafa dokar hana amfani da babura masu kafa biyu da masu kafa uku da aka fi sani da Napep, a fadin jihar a wani mataki na kare rayukan al'umma.

A cewar babban jami'i ga gwamnan jihar kan hulda da kafafen yada labarai, Abdu Labaran, gwamnatin ta yi haka ne saboda dalilai na tsaro.

Ya kara da cewa babban makasudin kafa dokar shi ne yaki da barayi da masu garkuwa da mutane da suke amfani da babur din wajen tafka ta'asa.

Labaran ya yi wa BBC karin bayani inda ya ce "an samar da dokar domin dakile irin ta'addancin da ake samu musamman garkuwa da mutane da ake yi a kan babura."

"Wannan doka ta dan wani lokaci ce ba wai doka ce ta dindindin ba" in ji Labaran.

Sai dai wannan mataki na gwamnati bai yi wa wasu jama'ar Katsina dadi ba musamman masu ababen hawa.

Wani matashi mai sana'ar babur a jihar ta Katsina, Nasiru Abdullahi Batsari ya ce duk da cewa akwai alfanu a sanya dokar amma a cewarsa, matakin zai takura wa al'umma musamman mutanen karkara.

Ya kara da cewa "Idan muka yi duba bayan lokacin da aka yi sasanci da barayin shanu, an saka dokar hana yawo da makami, wanda al'ummar gari sun daina yawo da makami"

"Kuma haka ya bai wa wadannan masu ta'addanci damar yawo da makamansu har suka kai yanzu suka canja suka koma satar mutane da kuma ci gaba da satar shanun da bata dukiyoyin al'umma." kamar yadda ya fada wa BBC.

Ya kara da cewa ba masu aikata ta'addanci ne kadai ke amfani da babura ba, "akwai mutane da suke amfani da babura da dama a jihar Katsina, wasu neman abinci suke, wasu kuma biyan bukatunsu na yau da kullum, wasu ma'aikata ne , sai sun tashi aiki da yamma ne suke hawan baburansu suke neman abin da za su rufa wa kansu asiri."

Sai dai ya yi maraba da dokar idan har za ta taimaka wajen yaki da matsalolin tsaron da jihar take fama da shi.

Akwai kuma rahotanni da suka ce wasu jama'a da suke fargabar cewa amfani da dokar za ta bai wa wasu jami'an tsaro damar cin zarafi da mutuncin al'umomin jihar.

Dokar hana hawa babur a arewacin Najeriya

Ko a baya-bayannan wasu jihohin Najeriya da ke yankin arewa musamman masu fama da kalubalen tsaro sun kafa irin wannan dokar.

Jihohin sun hada da Borno da Yobe da suka kafa dokar tun shekarar 2011 domin yakar Boko Haram.

Sauran sun hada da Kano da Zamfara da Kebbi da Sokoto da Kaduna da kuma Neja da su ma suke da irin wannan dokar amma dokar ba ta bai daya ba ce ba.

Labarai masu alaka