Ni ban ga abin fargaba ba game da Amotekun- Oba Hammed Makama
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ban ga abin fargaba ba game da Amotekun – Oba Hammed

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A baya-bayan nan ne gwamnonin kudu maso yamma na Najeriya suka sanar da kudirinsu na kafa kungiyar tsaro ta Amotekun.

Kafa rundunar tsaron ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar inda wasu ke ganin za ta iya zama barazana ga Najeriya a nan gaba.

A farkon makon nan ne gwamnatin Najeriya ta sanar da haramta kungiyar tsaron.

Sai dai Oba Hammed Makama, wanda shi ne Alafin na Kuta ya ce shi bai ga abin tashin hankali ba da kafa wannan rundunar.

Ya kara da cewa wannan tsari zai taimaka wa gwamnatin tarayya ne wajen samar da tsaro da ya zame mata wani al'amari mai wuya.

Labarai masu alaka