Lauyoyin Trump sun bukaci a wanke shi da gaggawa

Shugaba Donald Trump Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana zargin Shugaba Trump da amfani da matsayinsa wurin cimma burinsa na siyasa, a lokacin da ya bukaci Yukren ta binciki abokin hamayyarsa na jam'iyyar Democrats Joe Biden.

Tawagar da ke kariyar Shugaban Amurka Donald Trump a kan shariar tsige shi ya bukaci majalisar dattawa da ta yi gaggawar wanke shi.

Lauyoyin sun kira zaman da za a gudanar ranar Talata a matsayin 'hatsari ga kundin tsarin mulki'.

To sai dai a lokaci daya, majalisar wakilan Amurkar ta mika wani rahoto a gaban majalisar dattawan inda ta bayyana cewa abinda shugaban yayi cin hanci da rashawa ne.

Da yammacin yau Talata ne za a fara zaman sauraraen hukunci tsige Mr Trump din da majalisar wakilan ta yi a zauren majalisar dattawa.

Anan ne za a saurari korafin duka bangarorin kafin zuwa mataki na gaba.

Ana zargin Shugaba Trump da amfani da matsayinsa wurin cimma burinsa na siyasa, a lokacin da ya bukaci Yukren ta binciki abokin hamayyarsa na jam'iyyar Democrats Joe Biden.

Laifi na biyu shine kawowa majalisa tarnaki a lokacin da ta ke bincikensa.

Sanatocin za su shafe kwanaki shida na ko wane mako suna sauraren kararrakin.

Wannan shine karo na uku a tarihin Amurka ana tsige shugaban kasa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sanatocin za su shafe kwanaki shida na ko wane mako suna sauraren kararrakin

Lauyoyin sun gabatar da wani kundi da ke da shafuka 171 dauke da hujjojin da ke musanta cewa shugaban ya aikata ba dai dai ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa alkalin alkalan Amurka John Roberts ne zai jagoranci zaman.

Masana na gamnin cewa ko ya ta kaya, zai yi wuya a iya samun kashi biyu bisa uku na kuriun 'yan majalisar dattawan su dari, ganin cewa 'yan jam'iyyar Republican da shugaban ya fito ke da rinjaye.

To sai dai yayin da ake shirin fara wannan zama, tuni Mr Trump yayi nasa shirin na halartar taron tattalin arziki da za a yi a birnin Davos na Switzerland.