An so bai wa hammata iska a majalisa kan Trump

Mitch McConnell left the Senate as proceedings ended in the early hours Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai Mitch McConnell

Majalisar dattawan Amurka ta amince da wasu ka'idoji da aka gindaya kan fara sauraron shari'ar da za ta iya kai wa ga tsige Shugaba Donald Trump bayan kusan shafe sa'oi 13 ana tafka muhawara a ranar farko.

Masu gabatar da kara na jam'iyyar Democrat da lauyoyin Trump sun kusa bai wa hammata iska game da zaman sauraron shari'ar yayin da 'yan Republican suka nuna kin amincewarsu da bukatar a gabatar da shaidu fiye da daya.

Trump shi ne shugaba na uku da ya taba fuskantar barazanar tsigewa daga kan karagar mulki.

Ana tuhumarsa da yin gaban kansa da kuma yi wa yunkurin majalisa na gudanar da bincike karen tsaye amma ya musanta zargin.

Trump dai na fuskantar irin wannan shari'a ce bayan da majalisar wakilan kasar ta tsige shi a watan da ya gabata sakamakon samun sa da aikata laifukan da aka zarge shi da aikatawa.

Amma ba a sa ran majalisar dattawa wadda jam'iyyar Republican ke da rinjaye ta samu Trump da laifi har ma ta kai ga ta tsige shi.

A taron tattalin arziki na duniya a Davos da ke Switzerland, Trump ya yi watsi da zarge-zargen da ake masa inda ya ce "abin dariya ne" ma.

Me zai faru?

Sanatoci sun karbi rantsuwar zama alkalai masu gaskiya a zaman shari'ar da alkalin alkalan Amurka, John Roberts zai jagoranta.

'Yan Democrat da ke majalisar wadanda ake kira da "masu kula da batun tsigewa" za su kasance masu gabatar da kara yayin da tawagar shari'ar Trump za ta kasance masu kare kai.

Karkashin dokokin da aka gindaya a ranar farko a zaman da aka kammala da kusan karfe 02:00 agogon Amurka ranar Laraba, kowane bangare zai samu kamar sa'a 24 ya gabatar da bayanai cikin kwana uku.

Bayan haka kuma, a farkon makon gobe, sanatoci za su samu damar yin tambayoyi inda su kuma aka ba su sa'a 16.

Daga nan kuma hankali zai karkata ga babban batun sabbin masu shaida da hujjoji.

'Yan Democrat suna son ji daga bakin manyan ma'aikatan fadar White House da ke aiki da Shugaba Trump har da mukaddashin Shugaban Ma'aikata a fadar shugaban kasa Mick Mulvaney da kuma tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro John Bolton.

Sai dai akasarin 'yan Republican ba sa son hakan ta faru.

Yadda aka kada kuri'a ranar Talata

Bisa yadda jam'iyyun biyu suka kada kuri'a da kuri'u 53 da 47, majalisar dattawa ta yi watsi da wasu kudirori uku na 'yan Demokrat kan samun takardu da hujjoji a shari'ar tsigewar.

Sanatoci sun ki amince wa da wani kudiri daga shugaban marasa rinjaye Chuck Schumer na neman izinin samun wasu takardun Fadar White House da suka danganci yadda Trump ya yi mu'amala da Ukraine.

Sun kuma yi watsi da matakin bin diddigin na neman takardar izinin tattara bayanai da takardu daga ma'aikatar harkokin wajen Amurka da kuma ofishin kudi na fadar White House.

Sanatoci 'yan Republican sun kuma juya baya ga kokarin da' yan jam'iyyar Democrat ta yi na neman izinin Bolton, wanda ya ce zai girmama duk sharudan da aka sanya.

Labarai masu alaka