Ana neman a haramta tiyatar dawo da budurci

Akalla asibitoci 22 ne ke aikin dawo da budurci a Birtaniya Hakkin mallakar hoto Getty Images

Masu fafutuka na neman gwamnati ta hana aiwatar da tiyatar dawo da budurci baki daya.

Yawancin mata Musulmai na fuskantar barazanar amsa kiran sunan mazinata ko ma hallaka su idan aka gano sun taba aikata zina.

Saboda haka ne wasun su ke zabar yi musu tiyata don dawo musu da dumbarun farjinsu.

Sai dai ana fargabar cewa matakin haramtawar zai iya zama hadari ga mata Musulmai, domin za su iya komawa aikata hakan ta bayan fage.

Shawarwarin da kungiyar likitoci ta (GMC) ta bayar sun kunshi neman karin bayani daga wadanda suka kamata kafin kafin aiwatar da aikin.

'Rayuwa cikin tsoro'

Halaleh Taheri, wadda ta kirkiro kungiyar mata ta Gabas Ta Tsakiya ta bai wa BBC labarrin yadda wata daliba 'yar asalin kasar Moroko ke boye a Landan, bayan an fada mata mahaifinta ya yi hayar wani don kashe ta.

Bayan zuwan ta Birtaniya a 2014 don yin karatu, yarinyar wacce a yanzu ta kai shekara 26 ta samu saurayi kuma yanzu haka suna ci gaba da rayuwa tare.

Amma bayan da mahaifin nata ya ji labarin dangantakarsu da mutumin, sai ya nemi ta koma Moroko, inda ya kai ta asibiti don "gwajin matancinta" ya kuma gano an gusar da budurcinta, abinda yasa ya soma yunkurin raba ta da duniya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ta koma Landan, sai dai yanzu a ko da yaushe tana cikin tashin hankalin ko mahaifinta zai gano inda take zaune.

Wata 'yar Moroko da a yanzu ta shafe shekara 40 a duniya ta fada wa BBC cewa, an tilasta mata yin tiyatar dawo da budurcinta tun tana 'yar shekara 20, amma a yanzu ba za ta iya tursasa wa yaranta domin su yi ba.

"Ba zan taba iya musu hakan ba. Zan yi kokari in koya musu samun 'yancinsu".

Daren tarewa

Akwai a kalla asibitoci 22 da ke yin irin wannan tiyata.

Suna karbar fam 3,000 a matsayin kudin yin aikin da suke yi a sa'a guda kacal.

Masu fafutukar kare hakkin mata sun bayyana cewa irin wadannan asibitocin na cin riba da matan Musulmai, wadanda ke tsoron abin da ka iya faruwa idan aka gano cewa an "kau da budurcinsu" kafin daren aurensu.

Yawancin asibitocin kan ba da bayanan yadda suke yin aikin a shafukansu na intanet, abinda yasa cibiyar kula da matsalolin da suka shafi mata a Landan ke jan hankalin irin wadannan mata da su kaucewa duba irin wadannan shafuka.

BBC ta tuntubi irin wadannan asibitoci domin jin martaninsu, sai dai har kawo yanzu sun ki cewa ko uffan.

'Mummunar al'ada'

Sakataren harkokin lafiya Matt Hancock ya ce zai gudanar da bincike kan yadda za a daina wannan "mumunar al'adar", sai dai sashen kiwon lafiya bai ce komai ba kan yadda za a iya cimma burin hana wannan abu.

Sai dai Misis Taheri ta ce: "Mata na iya mutuwa a karshe idan ba a yi kyakkyawan tsari wajen hana yin tiyatar ba.

Dakta Khalid Khan, farfesa kan kiwon lafiyar mata a Barts da kuma makarantar koyar aikin likita da ke Landan, wanda kuma ganau ne kan yadda ake tiyatar, ya ce "sanya dokar hana tiyatar dawo da budurci ba shi ne mafita ba.''

Ya ce matsawar za a yi wa masu bukatar yi musu aikin cikakken jawabi game da yadda al'amarin yake to zai zamana dabara ta rage ga mai shiga rijiya.

''Na yi imanin cewa da zuciya daya liikitoci ke wannan aiki, domin kawai su kare irin wadannan mata daga gamuwa da cin zarafi".

'Tiyatar bata da wani alfanu'

Dakta Naomi Crouch, shugabar kungiyar kula da cututtukan yara da kuma matsalolin da suka shafi mata matasa na Birtaniya, ta nuna damuwa game da yadda ake tilastawa mata yin wannan tiyatar da "ba ta da wani alfanu".

Ta ce: "Kungiyar likitoci ta fayyace aikin da likitoci za su yi''.

"Mu a matsayinmu na ma'aikatan lafiya, mun yi rantsuwa tare da daukar alkawarin cewa ba za mu cutar da majinyata ba, kuma duk wani aiki da za mu yi da ya shafi hakan, a bayyane yake a kan ma iya bincikawa a gani.

Colin Melville, wani likita ne kana daraktan wayar da kai a kungiyar likitoci ta GMC, ya ce yana da muhimmanci a ce likitoci na lura da hadurran da majiyyata za su iya fuskanta a sakamakon yi musu aikin.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ya ce: "idan har tilastawa mutum aka yi ya yi tiyatar, ba lallai ne a samu amincewarsu kai tsaye ba. Idan likita ya gano cewa yarinya ko matashiya ba ta so a yi mata tiyatar, to kar a aikata hakan".

Wani abu sabo da ake yi wa farjin kuma shi ne 'labiaplasty', bi ma'ana tsuke bakin mashigarsa, ko kuma sauya masa fasali zuwa duk yadda aka so.

Daya daga cikin masu fafutukar da ake kira Taheri ta ce: "Irin wadannan mata na kallon kawunansu a matsayin masu ababen more rayuwa maimakon kallon kansu a matsayin 'yan adam.

"Ga matan Musulmai, suna yin hakan ne don gudun jin kunya da kuma tsoron hukunci."

"Ga wasu kuwa, rashin gamsuwa da yadda jikinsu yake ne, da kuma bin abunda al'umma ke fada musu kan cewa hakan daidai ne."

Labarai masu alaka