Najeriya na cikin halin yaki - Fadar shugaban kasa

Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto Buhari Sallau
Image caption Masana harkokin tsaro na ganin ci gaba da kasancewar hafsoshin tsaro a kan mukamansu na ta'azzara hare-hare.

Fadar shugaban Najeriya ta ce abin da ya sa Shugaba Muhammadu Buhari bai yi sauyin manyan hafsoshin tsaron kasar ba shi ne, saboda kasar na cikin halin yaki.

Mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da BBC a ranar Alhamis.

Kakakin shugaban kasar na martani ne ga masu kira da a sauya manyan hafsoshin tsaron kasar da suka shafe shekaru suna jagoranci, abin da ba kasafai aka saba gani ba.

Kazalika maganganunsa martani ne ga shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan kasar Sanata Eyinnaya Abaribe, da ya nemi shugaban ya yi murabus saboda gaza shawo kan matsalar tsaro a zaman majalisar na ranar Laraba.

Garba Shehu ya ce "Duk masu kushe ko suka kan manyan jami'an tsaron nan ba sa la'akari da cewa ko an ki ko an so Najeriya a cikin halin yaki take a yanzu.

"A matsayin Shugaba Buhari na tsohon janar a soja, yana sane da lokacin da ya kamata ya yi canjin kwamandoji da kuma lokacin da bai kamata ba."

Sannan mai magana da yawun shugaban kasar ya ce, Najeriya ta samu kanta a wannan hali ne tun bayan fantsamar kungiyar IS wadda ta faro daga Iraki da Syria, da kuma rikicin Libiya.

"Amma abin lura shi ne kowa ya san cewa Shugaba Buhari na bakin kokarinsa don kare rayuwa da dukiyar 'yan kasar nan tamu."

Daga cikin masu sukar gwamnatin game da gaza shawo kan matsalar tsaro har da babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, da ke cewa matsalolin da al'ummar kasar ke fuskanta ta bangaren tsaro a yanzu ba ya rasa nasaba da yadda gwamnati ke tafi da mulki.

Saurari hirar BBC Hausa da Garba Shehu ta hanyar latsa lasifikar da ke kasa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da Garba Shehu kan taron Buhari da hafsoshin tsaro

Me ya sa ake son cire su?

Neman sauya hafsoshin tsaron na da nasaba da karewar wa'adin aikinsu da ci gaban matsalolin tsaron kasar da kuma karin asarar da ake yi wurin yakar matsalar.

Daga cikin masu neman Buhari ya sauke manyan jami'an tsaron akwai masu kafa hujja da gazawarsu wajen magance matsalolin tsaron da suka dade suna addabar kasar.

A fahimtarsu, rashin tsaro a kasar wanda shi ne akin da aka nada su su samar ya isa a sallame su a nada sabbi da za su iya magance matsalolin.

Suna ganin zaman shugabannin tsaron babu amfanin da zai iya yi wa kasar sai ma ci gaban matsalolin.

Wasu masu sharhi kuma na cewa tun da har hafsoshin tsaron sun yi iya bakin kokarinsu wajen amfani da dabarunsu ba tare an samu nasara ba, ya kamata a maye gurbinsu da sabbin jini da za su gwada irin fasaharsu wajen tunkarar matsalolin.

Masu fahimtar na ganin ba wa sabbin jinin mukaman zai taimaka wajen daukan sabbin matakai da suka dace da matsalolin tsaro na zamani da kuma daukar karin mataka ia kan wanda na yanzun suka yi.

Akwai kuma masu cewa tun da har wa'adinsu ya kare to ya kamata su tafi domin wasu ma su samu irin damar.

Wa'adinsu

A watan Yulin shekarar 2015 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara nada manyan hafsoshin tsaron kasar guda hudu na tsawon shekara hudu bayan shugaban ya sauke magabtansu.

Shugaban ya nada su ne tare da mai ba shi shawara kan tsaro Janar Babagana Monguno mai murabus.

A shekarar 2019 shugaba Buhari ya tsawaita wa'adin hafsoshin tsaron da wata shida wanda ya kare a watan Dismban shekarar.

Su wane ne hafsoshin tsaron Najeriya?

Manyan hafsoshin tsaron su ne:

  • Manjo Janar Abayomi Gabriel Olonishakin - Babban hafsan hafsoshi.
  • Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai - Babban hafsan sojin kasa
  • Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas - Babban hafson sojin ruwa
  • Air Vice Marshal Sadiq Abubakar - Babban hafson sojin sama.
  • Air Vice Marshal Monday Riku Morgan - Shugaban rundunar tara bayanan sirri
  • Manjo Janar Babagana Monguno mai murabas - Mai bayar da shawara kan tsaro.

Me doka ta ce?

Wing Commander Musa Salmanu mai ritaya ya shaida wa BBC cewa ci gaba da zamansu bai saba ka'ida ba.

Ya ce dokar aikin soji ta ba wa shugaban kasa daman nada hafsoshin tsaro na wa'adin shekara biyu kuma shugaban na da hurumin sabunta masu wa'adin.

Don haka ba a karya wata doka ta tsarin aikin sojin kasar ba.

"A yanzu yadda muke babu dokar da aka karya ko da ko za a bar su su shekara ashirin ne," a cewarsa.

Matsalolin tsaron Najeriya

Matsalolin tsaron da ke addabar Najeriya sun yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a kasar baya ga asarar dukiyoyi da raba mutane da muhallansu

Boko Haram

Rikicin kungiyar Boko Haram da ta shafe shekara 10 tun daga 2009 tana kai hare-hare a sassan kasar musamman yankin arewa maso gabas.

Yanzu kungiyar ta yi rassa inda wani bangare da ya balle daga cikin kungiyar ya bayyana mubaya ga kungiyar IS da reshensa nahiyar Afirka wata ISWAP.

Kungiyoyin biyu sun na yin garkuwa da dubban mutane ciki har da 'yan makaranta da mata da kananan yara da tsofi, inda a wasu lokuta suke bautarwa da matan ko aurar da su ga mayakansu.

Suna kuma amfani da wasu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su musamman 'yan mata da kananan yara wajen kai harin kunar bakin wake.

Takun saka da 'yan Shi'a

Wata babbar matsalar tsaron a ganin wasu masu sharhi ita ce takun sakar da gwamnati ke yi da 'yan shi'a na IMN.

Kungiyar ta mabiya Shaikh Ibrahim El-zakzaky na cewa ita mai son zaman lafiya ce, sai dai gwamnati ta haramta kungiyar kuma ta sanya ta a cikin masu barazana ga tsaron kasa.

Gwamnati na ci gaba da tsare shugaban kungiyar wanda ta gurfanar a kotu da zargi da tayar da zaune tsaye, bayan 'yan kungiyar sun iy dauki ba dadi da sojoji.

'Yan kungiyar na zargin zalunci a tsare sheikh Ibrahim Zakzaky, kuma suna gudanar da zanga-zangar neman a sako shugaban nasu.

Garkuwa da mutane

Akwai kuma matsalar masu satar mutane domin karbar kudin fansa musamman a arewa ta yamma.

Matsalar garkuwa da mutane musamman a kan manyan tintuna ciki har da titin zuwab babban birnin tarayya ya yi ajalin mutane da dama ciki har da manyan sarakuna da jami'an gwamnati.

Neman ballewa

'Yan tayar da kayar baya irin kungiyar IPOB me neman ballewa daga kasar na daga cikin matsalolin da kasar ke fama da su.

Hakan ya yi sanadiyyar ayyana kungiyar a matsayin 'yar ta'adda tare da daukan matakan soji a kanta.

Gwamnatin kasar na kuma zargin jagoran tafiyar wanda ake shari'a da shi da cin amanar kasa.

Rikicin manoma da makiyaya

Yankin arewa na fama da rikicin manoma da makiyaya musamman a jihohin arewa ta tsakiya.

Hakan ya sa har yanzu ake zaman doya da manja tsakanin wasu al'ummomin yankin a jihohin Nassarawa, Benue, Taraba da sauransu.

'Yan bindiga dadi masu kai hare-hare a kauyuka da barayin shanu sun tilasta wa mazauna gudun hijira don tsira da ransu tare da hana su noma.

Fashi da makami

Fashi da makami wanda bai kebanta da wani yanki na kasar ba.

Sai dai ana iya tuna cewa yana daga cikin matsalolin tsaron da suka ritsa da wani janar din soja, Janar Idris Alkali a hanyarsa ta tafiya inda maharan suka kashe shi suka kuma jefa gawarsa a cikin rijiya.

Kazalika 'yan fashi da makami sun harbe tsohon babban hafsan tsaron kasar Alex Badeh a hanyarsa ta wata tafiya a jihar Nasarawa.

Fashi a teku

Masu fashi a tekun da ke kusa da kasar na daga cikin matsalolin wanda ya sa kasar kawance da kasashe makwabta na yankin Guinea domin yakar ayyukan bata garin.

Iyakokin kasar

Rashin isasshen tsaro a kan iyakokin kasar na daga abubuwan da ake ganin sun taimaka wa ayyukan bata gari da rashin tsaro a kasar.

Ana zargin karancin tsaro a iyakokin ya bayar da dama ga masu fasakwauri da safarar miyagun kwayoyi da makamai cin karensu babu babbaka.

Ya zuwa yanzu gwamnatin kasar ta rufe iyakokinta na kan kasa a wani mataki na inganta tsaro a kasar da dakile ayyukan bata gari da kuma bunkasa harkar kasuwancin kayan cikin gina.

Abin da gwamnatin ke cewa:

Gwamnatin kasar da rundunar sojin kasar sun cewa sun gama da Boko Haram, amma har yanzu kungiyar na kai hare-hare a yankin arewa masu gabas da iyakokin kasashe da ke makabtaka da kasar.

A wani jawabi da shugaban kasar ya yi a cikin makon nan, ya bayyana mamaki cewa har yanzu kungiyar na nan.

Matakan da aka dauka

Gwamnatin dai ta sha cewa tana iya kokarinta domin yaki da matsalolin satar mutane musamman a wasu jihohin arewa masu yammacin kasar da suka hadar da Zamfara da Katsina da kuma jihar Niger.

A jihohi irin Zamfara da a baya ta yi kaurin suna game da satar mutane ana ganin daukar matakan soji da sulhun da gwamnatin jihar ta yi da maharan ya taimaka wajen kawo sauki.

Hakan ya sa makwabciyarta Katsina ta bi sahu. Sai dai har yanzu akan samu hare-hare daga wadansu da gwamantocin jihohin ke cewa bata gari ne da suka yi watsi da sulhun.

A jihar Benue da Nassarawa da Filato daukar matakan soji sun taimaka wajen kawo raguwar rikicin manoma da makiya da satar shanu, amma har yanzu da sauran rina a kaba.

Ana samun hare-hare da daukar fansa jefi-jefi duk da wadannan matakan da aka dauka. Amma gwamnatocin jihohin na cewa suna iya bakin kokarinsu.

Dakarun gwamanti sun sha kwato mutane daga masu garkuwa da mutane, amma har yanzu ba a kawo karshen matsalar ba.

Matsalar fashi da makami da a baya ake ganin ya lafa a arewa, a baya-bayan ya ritsa da da tawagar basarake mai daraja ta daya a hanyar Kano zuwa Kaduan.

Ana iya cewa matakin sojin da sojojin kasar suka dauka game da 'yan fashin teku na taimaka wajen raguwar garkuwa da jiragen ruwa da baki a kan teku da ma ayyukan masu fasa bututun mai da tace mai ba bisa ka'idaba.

Hakan ya kuma yi tasiri wajen yayyafa wa yunkurin masu neman ballewa na Biyafara ruwa, bayan jerin gwanon ayyuka na musamman da sojoji suka yi a yankin.

Matakin da gwamnatin kasar ta dauka na bayar da lasisi ga kananan matatun mai na cikin gina shi ma ya taimaka wajen raguwar ayyukan haramtattun matatun mai a yankin kudu.

Sai dai har yanzu wasu 'yan kasar na ganin matakan basu haifar da sakamakon da ake bukata ba don haka dole sai an sake dabaru da shugabancin tsaron kasar.