Iska mai karfi ta rusa wani bangare na katangar Trump ta Mexico

A construction crew works on a fallen section of the US-Mexico border wall as seen from Mexicali, Baja California state, Mexico Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu gini na kokarin gyara bangaren da ya fadi din

Wata iska mai karfi ta rusa wani bangare na katangar da Shugaba Donald Trump ke ginawa a kan iyakar kasarsa da Mexico don yin shinge, a cewar jami'an Amurka.

Karafan da aka gina katangar da su sun zube a garin Calexico na California a ranar Laraba da safe.

Har zuwa lokacin da katangar ta zube, kankaren da aka yi don dora turakun katangar mai tsayin kamu 30 bai kammala bushewa ba.

Hukumar Kula da Yanayi ta Amurka ta ce a lokacin da abin ya faru ana wata iska mai gudun kilomita 48 cikin sa'a daya ne.

Katangar dai na cikin wani shiri da gwamnatin Trump take yi a kokarinta na hana bakin haure shiga Amurka ta kan iyakar Mexico.

A ranar Talata ne Mista Trump ya yi wani "kuri" a wajen wani taro a New Jersey cewa aikin ginin katangar na tafiya cikin sauri.

Kwana daya bayan nan, sai iska mai karfi ta rusa wani bangare na katangar da aka girke turaku da ke fuskantar bishiyoyi a kan wani titi a garin Mexicali, da ke kan iyakar Mexico.

"Sai dai cikin sa'a, hukumomin Mexico sun yi gaggawar shawo kan lamarin ta hanyar karkatar da ababen hawa daga kusa da titin," a cewar jami'in sintiri na kan iyaka na Amurka Carlos Pitones, kamar yadda ya shaida wa Jaridar LA Times.

Mista Pitones ya ce, "Ba a samu asarar dukiya ko jikkata ba."

Hotunan kan iyakar sun nuna yadda kugiyar daukar kayan aiki dauke da wadanda ke kokarin gyara katangar ta karkace.

A yayin da ya kai ziyara don ganin aikin ginin katangar a bara a California, Mista Trump ya bayyana kankaren da turakun da cewa masu karfi ne da ba za su iya rushewa ba.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
BBC Newsround ta je kan iyakar Amurka da Mexicon don ganin yadda shirin ginin katangar ke tafiya
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamnatin Trump ta ce an gina kusan mil 100 na sabuwar katangar

Labarai masu alaka