Mun yi wa Kwankwaso ritayar dole a siyasa - Ganduje

Gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje Hakkin mallakar hoto Alamy

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bugi kirjin cewa sun yi wa tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ritaya a siyasance.

Gwamna Ganduje, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Abba Anwar ya fitar, ya yadda cewa jam'iyyar PDP da tsohon gwamnan ke jagoranta a jihar ta gaza tabuka wani abun azo a gani yayin zabukan da aka yi a karshen mako na 'yan majalisar tarayya da na jihohi.

Gwamna Ganduje ya kara da cewa "shi kansa Kwankwaso ba shi da wani katabus a siyasar jihar a yanzu."

Abdullahi Umar Ganduje na wadannan kalamai lokacin da ya karbi bakuncin shugaban majalisar dokokin jihar Abdul'aziz Garba Gafasa a fadar gwamnatin jihar lokacin da yaje gabatar masa da 'yan majalisar jihar da suka samu nasara a zaben da ya gudana.

A cewar Ganduje ''Mun musu tayin su zo a hada hannu da su domin cicciba jihar Kano zuwa tudun mun tsira, mun ji dadi da wasun su suka amsa wannan kira, kamar dan majalisar da aka zaba a jam'iyyar PDP da zai wakilci Kiru da Bebeji wato Datti Yako'',.

Akwai wasu rahotanni da ke cewa dan majalisar zai koma jam'iyyar APC don tsira da kujerarsa a 2023, sai dai babu tabbacin ko gaskiya ne, amma an gan shi lokacin da ya je kai wa gwamna Gandujen takardar samun nasara da hukumar zaben kasar ta ba shi, abin da ya janyo ake kyautata zaton hakan na iya kasancewa.

Dangantaka dai na ci gaba da tsami tsakanin tsohon gwamnan jihar Kwankwaso da kuma gwamna Ganduje, bayan zaben gwamna da aka gudanar a jihar na shekarar 2019, wanda 'yan jam'iyyar PDP ke zargin an tafka magudi a cikinsa.

A makon da ya gabata ne kuma wasu manyan na kusa da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ciki har da shugaban jam'iyyar PDP, Rabi'u Sulaiman Bichi, suka sauya sheka zuwa APC.

To sai dai Sanata Kwankwaso ya ce "dukkansu sun sauya shekar ne saboda suna son zama Kwankwaso amma sun kasa."

Ya kara da cewa "idan bayan mahaifansu babu wani mutum da ya yi musu gatan da na yi musu."

Hakkin mallakar hoto KNSG
Image caption Tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Rabi'u Sulaiman Bichi ya sauya sheka zuwa APC

Labarai masu alaka