Ko kun san ayyukan da za a iya yi da 'kudin da Abacha' ya wawure?

Tsohon shugaban Najeriya Janar Sani Abacha

Asalin hoton, Getty Images

Wani abu da galibin 'yan Najeriya suka yarda da shi - shi ne a matukar karancin ababen more rayuwa a sassa daban-daban na kasar.

Hakan ne ma ya sa 'yan kasar da dama ke tuhuma a kan abin da ake yi da kudaden da ake karbowa, wadanda ake zargin marigayi Janar Sani Abacha da boyewa a kasashen waje lokacin yana mulki.

Kudaden da ake yunkurin dawo da su a baya-bayan nan dai su ne wadanda aka ajiye a Amurka, wadanda suka kai dala miliyan dari uku, kwatankwacin Naira biliyan dari da takwas da miliyan dari tara.

A makon da ya gabata ne dai gwamnatocin Najeriya da Amurka suka rataba hannu a kan wata yarjejeniya don dawo da kudin, wadanda Amurkar ta ce an yi safarar su yayin da kuma bayan mulkin Janar Abacha, wanda ya rasu a shekarar 1998.

Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta ce marigayi Abacha da 'yan korensa sun wawure dukiyar 'yan Najeriya, sun kuma karya dokokin kasa-da-kasa ta hanyar boye kudaden.

Ministan shari'a na Najeriya Abubakar Malami ne ya wakilci gwamnatin Najeriyar wajen kulla wanan yarjejeniya.

Kudaden wani bangare ne na biliyoyin dalolin da ake zargin tsohon shugaban mulkin sojan ya kwashe ya jibge a kasashe da dama na duniya da suka hadar da Amurka da Switzerland da Liechtenstein.

Dala miliyan 300 ba kananan kudade ba ne, kudi ne masu yawa da za a iya yin ayyukan raya kasa da su a fadin Najeriya.

Kan haka ne a cikin wannan makala BBC ta yi nazari kan ko wadanne irin ayyuka ne za a iya yi da wadannan makuden kudade a Najeriya.

Kudaden satar da suka rage
Kudaden satar da aka dawo da su.
 • $2-5bn
  1998
  Kungiyar Transparency International ta kiyasta cewa marigayin ya sace tsakanin dala biliyan 2 zuwa 5
 • $750m
  1998
  A lokacin da Janar Abdulsalam Abubakar ke shugabancin Najeriya an bankado tsabar kudi da suka kai $750m daga wajen iyalan Abacha.
 • $64m
  2000
  Switzerland ta dawo da $64m.
 • $1.2bn
  2002
  Shugaba Obasanjo ya kulla yarjejeniya da iyalan Abacha, ta yadda Najeriya za ta iya samun $1.2bn.
 • $160m
  2003
  $160m aka dawo da su daga Jersey, British Isles. Mahukuntan Najeriya sun ce an samu $149m.
 • $88m
  2003
  Switzerland ta dawo da $88m
 • $461m
  2005
  Switzerland ta dawo da $461m.3m. Ministar kudin Najeriya Ngozi Okonja Iweala da kuma shugaban bankin duniya sun ce an samu $458m a asusun banki a Swiss.
 • $44m
  2006
  $44m.1m aka dawo da su daga Switzerland.
 • $227m
  2014
  Ma'aikatar kudi ta ce an dawo da $227m daga Liechtenstein.
 • $320m
  2017
  Za a dawo da su daga Switzerland.
 • $308m
  2020
  Amurka za ta dawowa da Najeriya dala $308m a karkashin bisa sharadin cewa za a yi amfani da kudin wajen gudanar da manyan ayyuka uku a kasar
 • $2-5bn
  1998
  Kungiyar Transparency International ta kiyasta cewa marigayin ya sace tsakanin dala biliyan 2 zuwa 5
 • $750m
  1998
  A lokacin da Janar Abdulsalam Abubakar ke shugabancin Najeriya an bankado tsabar kudi da suka kai $750m daga wajen iyalan Abacha.
 • $1.2bn
  2002
  Shugaba Obasanjo ya kulla yarjejeniya da iyalan Abacha, ta yadda Najeriya za ta iya samun $1.2bn.
 • $64m
  2000
  Switzerland ta dawo da $64m.
 • $160m
  2003
  $160m aka dawo da su daga Jersey, British Isles. Mahukuntan Najeriya sun ce an samu $149m.
 • $88m
  2003
  Switzerland ta dawo da $88m
 • $44m
  2006
  $44m.1m aka dawo da su daga Switzerland.
 • $461m
  2005
  Switzerland ta dawo da $461m.3m. Ministar kudin Najeriya Ngozi Okonja Iweala da kuma shugaban bankin duniya sun ce an samu $458m a asusun banki a Swiss.
 • $227m
  2014
  Ma'aikatar kudi ta ce an dawo da $227m daga Liechtenstein.
 • $320m
  2017
  Za a dawo da su daga Switzerland.
 • $308m
  2020
  Amurka za ta dawowa da Najeriya dala $308m a karkashin bisa sharadin cewa za a yi amfani da kudin wajen gudanar da manyan ayyuka uku a kasar

Majiya

Transparency International, Gwamnatin Najeriya, Bankin Duniya, Attorney General Report Jersey

Me zaa iya yiwa 'yan Najeriya da kudaden?

Wannan ita ce babbar ayar tambayar, domin da yawa daga cikin 'yan Najeriya na jin cewa an dawo da biliyoyin kudade ba tare da sun san abin da ake yi da ba.

Adamu Tanko, wani masanin kasa da tsare-tsare ne a Najeriya, ya bayyana wa BBC ayyukan raya kasa da za a iya yi da wadannan kudade.

Mun kalli abubuwan da suka fi muhimmanci ga rayuwar jama'ar Najeriya, musamman a bangaren lafiya da ilimi da kuma gina tituna da dai sauran su.

Gina manyan asibitoci 774 a kasar

Adamu Tanko ya ce za a iya gina babban asibitin kasa irin na birnin Abuja a kowacce karamar hukuma da ke Najeriya, "har ma manyan kananan hukumomi su samu guda bibbiyu."

Asalin hoton, Getty Images

Gina manyan makarantu

Za a iya gina makarantun firamare hade da na sakandire masu azuzuwa 30 a ko wacce karamar hukuma da ke fadin Najeriya har ma a samu canji.

Layin dogo

Adamu Tanko ya kara da cewa kudaden za su isa a samar da karin layin dogo irin na Kaduna zuwa Abuja.

Layin dogo a Abuja

"Sannan kuma kudaden za su isa a kewaye Abuja baki daya da layin dogo mai zirga-zirga a birnin," in ji shi.

Kwatankwacin kudin da kasafin 2020

Mun yi duba ga kudaden da aka ware wa wasu ma'akatun kasar a kasafin kudin shekarar 2020, kuma wani abu da muka lura da shi shi ne kudaden, wadanda yawan su ya kai Naira biliyan dari da takwas da miliyan dari tara sun fi abin da aka ware wa ma'aikatu kamar haka yawa :-.

 • Sun fi na Ma'aikatar Tsaro da aka warewa biliyan 98.87
 • Sun fi na Ma'aikatar Lafiya da aka warewa biliyan 90.98
 • Sun fi na Ma'aikatar Gona da Raya Karkara da aka warewa biliyan 79.79
 • Sun fi na Ma'aikatar Ruwa da aka warewa biliyan 78.34
 • Sun fi na Ma'aikatar Jinkai da Agajin Gaggawa da aka warewa biliyan 54.45
 • Sun fi na Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama da aka warewa biliyan 53.85
 • Sun fi na Ma'aikatar Kasuwanci da Masana'antu da aka warewa biliyan 41.34
 • Sun fi na Ma'aikatar Kimiyya da Fasaha da aka warewa biliyan 37.55.

Ayyukan kasafin kudin 2020 da kudin za su iya yi

Kazalika wadannan kudade da ake zargin tsohon shugaban Najeriyar Janar Sani Abacha ya jibge a Amurka za su iya yin ayyuka da dama da aka tsara gudanarwa a kasafin kudin Najeriya na shekarar ta 2020.

Ga yadda lissafin yake daki-daki kamar haka:-.

Ma'aikatar lafiya

 • Za a iya amfani da naira biliyan hudu da miliyan dari takwas wajen kaddamar da shirin yaki da cutar Polio baki daya
 • Za a iya amfani da biliyan hudu da ? wajen yaki da cututtuka a Najeriya
 • Za a iya amfani da naira biliyan arba'in da hudu da miliyan hamsin wajen aiwatar da shirin kula da lafiya na kasar
 • Za a iya amfani da naira biliyan biyu wajen inganta ayyukan ungozomomi a dukkanin asibitocin Najeriya.

Dukkanin wadannan ayyuka na sama za a iya yin su a kan naira biliyan hamsin da biyar da miliyan dari biyar, kwatankwacin rabin baki dayan kudin da Amurkar za ta dawo da su ke nan.

Ma'aikatar ilimi

 • Za a iya amfani da biliyan uku don samar da tsaro a kwalejojin ilimi 104 da ke fadin Najeriya
 • Za a iya amfani da biliyan biyu don aza harsashin ginin makarantun kimiyya da fasaha guda shida a dukkanin yankunan Najeriya
 • Za a iya amfani da naira biliyan hudu da miliyan tamanin da uku don aiwatar da shirin bayar da tallafin karatu daban-daban a fadin Najeriya
 • Za a iya amfani da naira biliyan daya da miliyan sittin da shida wajen biyan fiye da malaman makaranta dubu biyar da aka dauke su aiki bisa tsarin bayar da ilimi na gwamnatin kasar.

Dukkanin wadannan ayyuka za a yi su ne a kan naira biliyan goma sha daya da miliyan dari hudu da arba'in, ma'ana kasa da kashi 10 cikin 100 na kudaden.

Ma'aikatar wuta

 • Za a iya amfani da biliyan biyu wajen biyan kudin tashar samar da wutar lantarki ta Mambila.
 • Za a iya amfani da Naira miliyan dari biyu wajen samar da wutar lantarki mai karfin Megawatt 215, da kuma tashar samar da iskar Gas a Kaduna.
 • Za a iya amfani da Naira miliyan dari da hamsin wajen aiwatar da shirin Afam, na samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana

Dukkanin wadannan ayyuka, na wadannan ma'aikatu da ke sama za a yi su ne a kan naira biliyan sittin da bakwai da miliyan dari hudu da arba'in da hudu, ma'ana kwatankwacin kashi 60 cikin dari na kudaden da ake magana a kansu.

Asalin hoton, Getty Images

Matashiya

Tun bayan mutuwar tsohon shugaban mulkin soji, gwamnatoci a Najeriya suka soma bankado makudan kudaden da ya jibge a kasashen Turai kamar su Switzerland da Amurka da Liechtenstein da dai sauran su.

Babu wanda ya san dalilin da ya sa tsohon shugaban ya kai kudaden Turai, kuma har kawo wannan lokaci ana ci gaba da dawo da su lokaci zuwa lokaci ba tare da sun kare ba.

An jima ana zargin 'yan siyasar Najeriya da jibge kudaden kasar a Turai, domin lokuta da dama hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar, EFCC, na gano irin wadannan kudade, har ma a dawo dasu daga bisani.

Babu wanda ya san adadin kudaden jumlatan, amma har yanzu ana ci gaba da dawo da su.

Ina aka kwana?

Wani rahoto da hukumomin Najeriya suka fitar a kwanan baya ya nuna cewa daga shekarar 2008 zuwa 2019 kasar Switzerland kadai ta dawo wa Najeriya da dala biliyan daya, kwatankwacin naira biliyan dari uku da miliyan dari da sittin da uku.

Amma ita ma Amurka ta dawo da kudade masu yawa a baya, da sauran kasashen da kudin suke.

Wasu daga cikin 'yan kasar na da ra'ayin cewa tun lokacin da ake dawo da kudaden har ya zuwa yanzu, ba su gani a kasa ba.

A shekarar 2018, gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin raba wa wasu 'yan kasar da ke fama da talauci wani bangare na kudaden.

Daga bisani, a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin 2020 a gaban majalisar dokokin kasar, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta yi amfani da kudaden wajen aiwatar da ayyukan da ta tsara gudanarwa a kasafin kudin wannan shekara.

Asalin hoton, Getty Images

Dokokin da Amurka ta gindayawa Najeriya

Gwamnatin Amurka ta shardanta wa Najeriya cewa muddin ta bari aka sake sace kudin da take shirin dawo mata da su yayin aikin da aka tsara za a gudanar da su to sai ta biya.

A ta bakin mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar, Amurka ta shardanta cewa Najeriya za ta biya duk wani kudi da aka sace yayin gudanar da ayyukan raya kasa da aka karbo kudin dominsu, kamar yadda suka yi yarjejeniya.

Gwamnatin Najeriya ce ta wallafa wannan sanarwar a shafinta na Twitter.