Cikin Hotuna: Abubuwan da suka faru a Najeriya a makon nan
Wasu daga cikin abubuwan da suka faru a Najeriya a wannan makon.

A ranar Litinin ne mazauna jihar Legas suka yi cirko-cirko a gefen tituna sakamakon haramta baburan acaba da kuma keke napep da gwamnatin jihar ta yi
Gwamnatin jihar dai ta yi alkawarin cewa za ta sama wa jama'a wasu hanyoyin sufurin na daban
Asalin hoton, Nigeria Police
Rundunar 'yan sandan ta ce an harbi wani jirginta mai saukar ungulu a yayin harin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Sufeto Muhammed Abubakar da kuma 'yan bindiga 250. Babu wata kafa mai zaman kanta da tabbatar da faruwar hakan
Asalin hoton, Nigeria Police
A ranar Laraba rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kwato manyan makanai daga mayakan kungiyar Ansaru da kuma masu garkuwa da mutane a dajin Dukuru da ke Birnin Gwari a jihar Kaduna
Asalin hoton, Zainab S-Bagudu
Matan gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun hallara a birnin Maiduguri ranar Laraba domin yin taro.
Asalin hoton, Zainab S-Bagudu
Uwar gidan gwamnan jihar Kebbi, Hajiya Zainab Bagudu, ta ce matan gwamnonin sun yanke shawarar daukar nauyin jinyar wata mai suna Hafsat, wadda ke fama da cutar kansar nono albarkacin ranar yaki da cutar da aka gudanar a tsawon makon da ya gabata a fadin duniya
Asalin hoton, Presidency Nigeria
A ranar Juma'a ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin jiragen yaki masu saukar ungulu, wadanda gwamnatinsa ta sayo kuma ta bai wa rundunar sojin Najeriya
Asalin hoton, Presidency Nigeria
Gwamnatin Buhari ta bayyana cewa ta sayo jiragen yaki 22 tun bayan hawanta mulki a 2015, sannan kuma wasu 17 na kan hanyarsu ta zuwa Najeriya
Asalin hoton, Buhari Sallau
A ranar Juma'a ne Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci wata tawagar shugabannin al'umma a jihar zuwa fadar shugaban kasa, inda suka gana Muhammdu Buhari.
Asalin hoton, Buhari Sallau
Tawagar ta hada da 'yan siyasa da sarakuna da mawaka. Sarkin Bichhi, Alhaji Aminu Ado Bayero ne kadai ya samu zuwa a cikin sarakuna biyar na jihar...
Asalin hoton, Presidency Nigeria
...daga bisani a ranar ta Juma'a Shugaba Buharin ya isa Adis Ababa babban birnin kasar Habasha wato Ethiopia domin halartar taron shugabannin kasashen kungiyar hadin kan Afirka ta AU na 33.
Asalin hoton, Presidency Nigeria
Firai Ministan Habasha, Abiy Ahmed (tsakiya) ne ya tarbe shi a filin jrgin sama