Yadda aka yi bikin cikar Sarkin Zazzau shekara 45 a kan mulki

Hakkin mallakar hoto @amorsbakery
Image caption Hoton Sarki Shehu Idris a jikin kek na alfarma mai hawa uku, wanda yake da launin fari da ruwan zinare. An yi kek din na musamman ne domin bikin cikar sarkin shekara 45 yana jagorantar Masarautar Zazzau
Hakkin mallakar hoto @mlgkaduna
Image caption Sarkin Zazzau Alhaji Dr. Shehu Idris a lokacin bikin cikarsa shekara 45 a kan mulki ranar Asabar 8 ga watan Fabarairun shekarar 2020
Hakkin mallakar hoto Majeeda Studio
Image caption Yadda aka kawata rawanin wani mahayin doki da tambarin Arewacin Najeriya
Hakkin mallakar hoto Hakuri Photos and Majeeda Studio
Image caption Uban Garin Zazzau Alhaji Bashir Shehu Idris yayin hawan daba
Hakkin mallakar hoto @ghøst_alamin
Image caption Wani mahayin doki da ya bade fuskarsa da bula a wurin hawan dabar cikar Sarkin Zazzau Shehu Idris shekara 45 a kan karaga
Hakkin mallakar hoto @ghøst_alamin
Image caption Tawagar wasu mahayan dawaki a lokacin hawan dabar murnar cikar Sarki Shehu Idris shekara 45 a kan mulkin Masarautar Zazzau
Hakkin mallakar hoto Hakuri Photos and Majeeda Studio
Image caption 'Yan majalisar Sarkin Zazzau zagaye da mai gayya mai aiki kuma mai masaukin baki, Sarkin Zazzau Shehu Idris a ranar bikin
Hakkin mallakar hoto Hakuri Photos & Majeeda Studios
Image caption 'Yan bindigar Sarkin Zazzau
Hakkin mallakar hoto @AlheriSufyan
Image caption Masu wasa da wuta a lokacin bikin
Hakkin mallakar hoto Hakuri Photos and Majeeda Studio
Image caption Tawagar Magajin Garin Zazzau
Hakkin mallakar hoto @Abba_Ramalan
Image caption Sarkin Zazzau Shehu Idris na karbar gaisuwa daga talakawansa
Hakkin mallakar hoto Hakuri Photos & Majeeda Studio
Image caption Hagu zuwa dama: Ministan Muhalli Dr. Mohammed Mahmoud, Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris
Hakkin mallakar hoto Hakuri Photos and Majeeda Studio
Image caption Magajin Garin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli yana kai gaisuwa
Hakkin mallakar hoto Hakuri Photos & Majeeda Studios
Image caption Danruwatan Zazzau Alhaji Bello Shehu Idris
Hakkin mallakar hoto @GovKaduna
Image caption Sarkin Zazzau tare da Gwamnan Jihar Kaduna Nasir Ahmed Elrufa'i a wurin taron
Hakkin mallakar hoto Instagram/majeeda_studio
Image caption Sarkin Musulmi ya zauna kusa da Sarkin Zazzau Shehu Idris
Hakkin mallakar hoto Hakuri Photos & Majeeda Studio
Image caption Danmajen Zazzau Alhaji Nasiru Shehu Idris ya yi Hawan Daba
Hakkin mallakar hoto Hakuri Photos and Majeeda Studio
Image caption Uban Garin Zazzau Alhaji Bashir Shehu Idris yayin hawan daba
Hakkin mallakar hoto Arewaemag
Image caption Wasu daga cikin mahalarta taron
Hakkin mallakar hoto Instagram/majeeda-studio
Image caption Sarkin Zazzau Alhaji Dr. Shehu Idris a lokacin bikin cikarsa shekara 45 a kan mulki a ranar Asabar 8 ga watan Fabarairun shekarar 2020