Shin Buratai ya ce zai fallasa masu daukar nauyin ta’addanci?

'Yan Najeriya na so a cire hafsoshin soji ciki har da Buratai Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan Najeriya na so a cire hafsoshin soji ciki har da Buratai

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta bayyana labarin da ake yadawa cewa shugabanta ya sha alwashin fallasa masu daukar nauyin ta'addanci da cewa labarin karya ne.

Wata jarida ce ta wallafa labarin ranar Talata da ke cewa Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ya ce 'yan kasar za su yi matukar kaduwa idan ya fallasa masu daukar nauyin 'yan ta'adda.

Amma a wani sako da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce "Wannan labarin karya ne. Wannan labarin karya ne."

Hare-haren 'yan ta'adda dai na ci gaba da karuwa a kasar, lamarin da ya sa 'yan Najeriya suka kara kaimi wurin yin kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya cire hafsoshin sojin kasar, ciki har da Mr Buratai.

Ko a farkon makon nan, wasu da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutum fiye da 30 a garin Auno na jihar Borno.

Mayakan sun kai harin ne da tsakanin karfe 9 zuwa 10 na daren Lahadi yayin da matafiyan ke barci cikin motocinsu bayan jami'an tsaro sun hana su shiga birnin Maiduguri tun da misalin karfe biyar na yammaci.

Labarai masu alaka