Soyayyar shafukan sada zumunta? Ga hanyoyi bakwai na samun nasara

Wata matashiya rike da wayar hannu. Tana murmushi, ta sanya da doguwar riga mai launin rawaya ta tafiya a gabar wani rafi da almuru. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ya dace ka yi rijista da wata manhajar soyayyar intanet ... kuma yana da kyau ka tabbatar ka yi farin cikin samun irin wanda kake so

Shin ba ka da aure ne a wanann rana ta masoya kuma kana neman samun masoya?

Kimanin mutum miliyan 240 a fadin duniya na shiga intanet domin neman wadanda za su aura, a cewar Statista. Amma kana da masaniyar cewa wasu da dama ba su dacewa da kulla soyayya?

Ga wasu hanyoyin da za su taimaka maka wurin jan hankali da muka tattaro daga Zoe Strimpel mawallafiyar 'The Man Diet' da kuma da Suzie Hayman, kwararriyar mai ba da shawara kan zamantakewa.

1. Kar ka fara soyayyar domin 'birgewa'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Na farko: kar ka fara, matukar ba ka son ka yi

Idan ka ji ba ka so, ka daina. Idan ba ka son mutun kar ka ci gaba da hulda da shi.

'Jarabawa' na da hadari - tana wahalarwa da gajiyarwa tare da sa mana mummunan zato game da kanmu ko wasu.

2. Bi abin da zuciyarka da nutsu da shi

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Da zarar ka ji ba ka so ko ba ka aminta da wanda ka ke soyayya da shi ba - kar ka bata lokaci wajen daukar mataki

Idan ka fahimci akwai matsala, to kar ka yi wasa da ita.

Akwai yiwuwar ka yi ta tunanin cewa: 'Laifi na ne'. Babu mamaki su ne matsalar.

3. Bincike ya nuna cewa takaita aika sakonnin ya fi fa'ida

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nagarta ba yawa ba - takaitacciyar hira mai dadi za ta fi faranta rai fiye da doguwar hira mara ma'ana

Hira da daruruwan mutane a lokaci guda na iya gajiyar da kai.

Takaita zancenka zuwa ga mutanen da kake jin dadin yin hakan da su - wadanda ka fi ganin alamun tabbaci daga gare su.

4. Shiga wuraren da mutane suka fi yawa

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ka fi samun yiwuwar haduwa da wanda za ka so idan ka shiga taron jama'a, fiye da idan kana kai kadai - haka manhajar soyayya ta ke

Ka guji shiga dandalin musamman na soyayya - shiga wuraren da mutane suka fi yawa.

Daga cikin mutane kake samun wanda kake so, saboda a haka sai ka shiga wurin mutanen da suka fi yawa. Kar ka biye wa dandalin masu riya cewa suke da na gari zalla.

Ba za ta yiwu ba. Kuma babu wani yanke.

5. Farawa da neman abokai

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Farawa da abota na da kyau a batun soyayya

Alaka mafi kyau na kulluwa idan ta fara daga abota sannan ta rikide ta koma ta soyayya.

Akwai yiwuwar abokai su yi dalilin haduwar ka da masoyinka.

6. Kasance mai saukin kai

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Ba ka dace da ni ba ko kadan' - 'Kai ma haka!

Kana iya tunanin cewa ka san abin da ya fi birge ka amma...

Idan ka fiye tsuke zabinka, akwai yiwuwar ba za ka samu wanda ya dace da kai ba, saboda kawai ba shi da kamannin hakan a fuska.

7. Ka yi hattara da tsanaki

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Soyayyar intanet na iya kawo farin ciki - amma dole sai ka yi bincike sannan ka yanke wa kanka zabin da ya fi dacewa.

Babbar illar soyayyar intanet ita ce rashin cikakken masaniya game da juna, saboda kowannenku mutanen da ya sani daban suke da na dayan.

Yi hattara idan har ka ga alamun matsala ko rashin gaskiya.

Rokon kudi daga sabon masoyi - ko yawan saba alkawari - ya isa zama dalilin ka yanke alakar.

Kar ka jefa kanka cikin rashin tabbacin farin ciki a soyayya.


Wannan sako an fassara shi ne daga shirin abokan hulda na BBC wato You & Yours.