Matar shugaban Namibia za ta bayar da dukiyarta sadaka

Monica Geingos Hakkin mallakar hoto Getty Images

Uwargidan shugaban kasar Namibia ta yi alkawarin bayar da dukiyarta sadaka bayan ta mutu.

Monica Geingos, na da dukiyar da aka kiyasta cewa za ta kai dala miliyan uku, wadda aka ce ta tsara mika ta ga daya daga cikin gidauniyoyinta don tallafawa al'umma.

Gidauniyar ta kan bayar da tallafi ga masu kananan masana'antu, da bayar da tallafi ga dalibai marasa gata da kuma bayar da tallafi ga matan da aka ci zarafinsu.

Mai dakin shugaban kasar, lauya ce, wadda kuma take kare wadanda aka ci zarafi.

Kazalika ta musanta zargin cewa tana neman mukamin gwamnati.

Ms Geingos ta ce "Na yi amanna cewa gado na daya daga cikin babban abin da ke janyo rashin daidaito a tsakanin al'umma, shi yasa na yanke shawarar sadaukar da dukiyata ga mabukata".

Bayan shugaban Namibia Hage Geingob ya dare karagar mulki ne a 2015, kuma shi da matarsa Monica Geingos sun gabatar da dukiyarsu a lokacin da ta kai kusan dala miliyan takwas.

Sharhi: Aisha Shariff Baffa

Ba kasafai ake samun irin wannan abu ba matar shugaban kasa ta sadaukar da dukiyarta ga aikin alkhairi bayan ta mutu.

Yawanci dai mutane kan tara dukiya domin su bar wa magada, wala 'ya'yansu ko 'yan uwansu saboda ka da su kasance a cikin talauci.

Amma a bangaren mai dakin shugaban kasar Namibia, ta ce gado na daga cikin abin da ke haifar da rashin daidaito, shi ya sa tun kafin ta mutu ma ta sadaukar da dukiyar.

Abin tambayar a nan shi ne, shin ina 'ya'yanta?

Kuma ko hakan da ta yi zai zamo darasi ga sauran matan shugaban kasa ko kuma masu da hannu da shuni?

Labarai masu alaka