Kotun koli ta soke zaben gwamnan Bayelsa na APC

David Lyon and Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency

Kotun kolin Najeriya ta soke zaben gwamnan jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin kasar.

Kotun ta soke zaben David Lyon, na jam'iyyar APC mai mulkin kasar ne kwana guda kafin ya sha rantsuwar kama aiki.

Alkalan kotun biyar, wadanda Mai shari'a Mary Odili ta jagoranta wajen yanke hukuncin, sun ce sn soke zaben Mr Lyon ne saboda mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremienyo ya mika wa hukumar zaben kasar takardun bogi domin a bar shi ya tsaya takara a zaben ranar 16 ga watan Nuwambar da ya gabata.

A watan Nuwambar 2019, hukumar zaben kasar INEC ta ayyana Lyon na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan ranar 16 ga watan Nuwamba, bayan ya samu kuri'u 352,552.

Hakazalika hukumar zaben ta bayyana cewa Mista Douye Diri na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 143,172.