Mece ce Ranar Valentine; wadanne wurare ne aka haramta yin ta?

valentine Hakkin mallakar hoto Getty Images

Rana irin ta yau - 14 ga watan Fabrairun kowace shekara - ita ce Ranar Masoya Ta Duniya, wato Ranar Valentine.

Masoya a matakai daban-daban kan nuna kulawa ta musamman da tarairayar juna a irin wannan rana.

Kafin ta zama Ranar Masoya, Ranar Valentine rana ce da aka ware domin taimako da kyautatawa marasa karfi a cikin al'umma.

Valentine sunan wani mutumin kirki ne dan asalin ƙasar Girka da ya shahara da wadannan dabi'u na gari a karnin da suka gabata, kamar yadda tarihi ya nuna.

Ko da yake an sha bamban game da bikin Ranar Valentine ta fuskar al'ada da addini, amma masu bikin ranar daga mabiya addinai da al'adu da akidu daban-daban.

Faranta rai

Masoyan da ke bikin wannan rana kan shirya wa zuwansa domin kyautatawa da faranta wa wadanda suke kauna rai, tare da bayyana musu yadda suke kaunar su.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Valentine sunan wani mutumin kirki ne dan asalin ƙasar Girka da ya shahara da wadannan dabi'u na gari a karnin da suka gabata, kamar yadda tarihi ya nuna.

Kyaututtuka

Suna yi wa juna kyaututtuka da sakonni na musamman masu ban mamaki domin jaddada yadda kaunarsu take.

Kyaututtukan soyayya musamman jajayen furannin Rose wadanda suka shahara a matsayin tambarin so, su ne ake bayarwa a tsakanin masoya a irin wannan rana.

Kazalika masoya kan sanya kyaututtukansu a cikin kayatattun kwalaye ko jakkuna ko mazubai masu launin jan Rose domin alamta soyayya.

Bai wa juna lokaci

Ko da yake Ranar Masoya ba ranar hutu ba ce, amma ma'aurata da dadaddun masoya kan yi amfani da zarafin ranar su kebe wa kansu lokaci da ziyartar juna ko wasu wurare na musamman, domin yaukaka dankon soyayya da ke tsakaninsu.

Neman aure

Daga cikin marasa aure akwai masoyan da kan zabi Ranar Masoya a matsayin ranar mika bukatar neman amincewar masoyansu da su aure su.

Wasu kan gabatar da kansu a wurin surukai ko tura manya su nema musu aure a cikin irin wannan rana.

Akwai wadanda za su so daurin aurensu ko bikin ya kasance a irin wannan rana.

Sabbin masoya

A ranar kuma a kan samu mutanen da ke fara bayyana wa juna abin da ke cikin zuciyarsu na kauna wa wadanda suke so.

Sulhu

Wasu wadanda suka samu sabani a baya kuma kan samu sasanci tare da bude wani sabon babin soyayya da fahimtar juna a tsakaninsu daga Ranar Valentine.

Sabanin fahimta

Fahimta a kan Ranar Masoya ta bambanta ta fuskar akida da al'ada da kuma ra'ayi.

Gargajiya

Daga cikin jama'a akwai wadanda suka ci gaba da riko da gargajiyar Ranar Valentine inda suke yin ayyukan tallafi da nuna ga mabukata da marayu da sauransu.

Sharholiya

Akwai masu ganin Ranar Valentine al'adar Turawa ce da aka aro.

Sun kara da cewa ya duk da cewa asalin ranar abu ne mai kyau, amma yanzu an sauya makasudin ranar na kyautatawa da tausaya wa marasa karfi ta koma ranar yin sharholiya.

Suna masu cewa a yanzu bikin Ranar Valentine na taimakawa wajen yada miyagun al'adun Turai da ayyukan badala da lalata tarbiyya musamman a tsakanin matasa.

Don haka suke cewa Ranar Masoya ba ta dace ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kullum ranar Masoya ce

Wasu na da ra'ayin bikin Ranar Valentine ba shi da fa'ida domin nuna soyayya da kauna bai kebanta da wani lokaci ko rana ba.

"Kowace rana, rana ce ta soyayya domin a ko yaushe masoya na hakika na jin juna a ransu," a cewar wata mai irin wannan fahimtar.

"A don haka suke cewa bikin ranar tamkar wani yunkuri ne kayyade lokacin bayyana soyayya zuwa rana daya tal a shekara."

'Ya kamata'

Masu bikin ranar na ganin babu laifi a kebe wata rana ta bai daya ta yadda jama'a za su ke bayyana wa juna soyayya da nuna kulawa kamar yadda ake yi a ranar.

'Ya haramta'

A mahanga ta Islama kuma malamai sun bayyana haramcin bikin Ranar Valentine.

A cewarsu, haramcin bikin ranar na da nasaba da asalin ranar wanda ba shi da tushe a Shari'ar Musulunci.

Asalin ranar mabiya addinin Masihiyya na darikar katolika ne suka fara murnar ranar, don haka addininsu ne kuma bai halasta ga Musulmi ya yi addinin da ba Islama ba.

Yin bikin ranar a cewarsu, kwaikwayon wadanda ba Musulmai ba ne kuma Muslunci ya haramta yi hakan.

Malaman suka kara da cewa ana yada fasadi na fasikanci a ranar don haka yin bikin taimakawa yada barna a ban kasa ne wanda shi ma babban laifi ne.

Wuraren da ba a bikin Ranar Valentine

A wasu wuraren kuma hukumomi sun haramta bikin ranar saboda wasu dalilai.

A kasar Saudiyya mai amfani da shari'ar Muslunci, hukumar Hisba ta hana yin bikin Ranar Valentine, saboda ya saba wa addini.

Amma rahotanni daga kasar na cewa masu sayar da furanni kan kai wa masu bukata a cikin dare don guje wa fushin hukuma.

Sai dai a baya-bayan nan wasu sauye-sauyen da Yarima Mai Jiran Gado Mohammed Bin Salman ya kawo na sassauta wasu dokoki da suka shafi harkokin shakatawa da yawon bude ido a kasar sun sa ana ganin karfin hukumar Hisbar ya ragu sosai.

Sauran wuraren da aka hana yin bikin Ranar Masoya ta Valentine sun haɗa da kasashen Iran da Pakistan da yankin Ache na kasar Indonesiya masu aiki da Shari'ar Musulunci.