Rikicin Mali: Mutum 30 sun mutu a sabon rikici

Mali army insignia Hakkin mallakar hoto AFP

A Kalla mutum 30, ciki har da sojoji tara aka kashe a rikice-rikice daban-daban uku a Mali.

An kashe mutum ashirin da daya lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari wani kauye a tsakiyar Mali, kuma suka kona gidaje da amfanin gona da dabbobi.

Wasu sojoji takwas kuma sun mutu a wani kwanton bauna, yayin da aka kashe wani soja daya a wani hari da aka kai wani sansanin sojoji a yankin Gao.

Mali na fama da tashin hankali tun 2012 lokacin da wani rikicin 'yan tawaye masu tsattsauran ra'ayin addinin musulunci sya barke a arewacin kasar.

Kauyen Ogossagou, inda aka kai harin na ranar Juma'a, mazaunar Fulani ce wanda kuma mafi yawansu musulmi ne kuma makiyaya.

Sauran kabilu a Mali- ciki har da al'umar Dogon- sun zargi Fulani da hada kai da kungiyoyi masu ikirarin jihadi da ke aiki a yankin sahel.

Wannan zargin ya rura wutar rikicin kabilanci a 'yan shekarun nan.

A watan Maris din 2019, mutum 160 aka kashe a wani harin a Ogossagou, wanda hukumomi suka zargi mayakan Dogon da aikatawa.

Harin ya janyo zanga-zanga da dama bisa zargin gwamnati da nuna halin ko-in-kula, da kuma firayim ministan Mali na wannan lokacin, Soumeylou Boubèye Maïga ya yi ritaya daga baya.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin na baya-bayan nan, amma mai garin Cif Aly Ousmane Barry ya shaida wa kafofin yada labaran kasa cdwa 'yan bindigar sun kai harin ne sa'o'i bayan da dakarun gwamnati suka janye daga yankin.

Tun shekarar 2012, dakarun Mali sun yi kokarin karbo ikon yankuna da dama da mayakan suka kwace tare da taimakon Faransa, wadda ta tura sojoji 4,500 zuwa yankin.

Majalisar Dinkin Duniya na da dakarun wanzar da zaman lafiya 13,000 a Mali.

Amma an rasa rayuka da dama a Mali kuma kasar na fama wajen shawo kan matsalar wanda ya bazu zuwa Burkina Faso da Nijar.

Ana ganin yaki da 'yan bindiga a yankin Sahel na da matukar muhimmanci don tabbatar da tsaro a fadin yankin da ma nahiyar Turai.

Ministar wajen Faransa, Florence Parly ta je Washington a cikin watan jiya da burin jawo ra'ayin Amurka ta ci gaba da taimakawa ta fannin samar da jirage marasa matuki da bayanan sirri da sufuri- wanda ta ce na da matukar muhimmanci ga ayyukan sojojin Faransar.

Labarai masu alaka

Karin bayani