Cikin hotuna: Abubuwan da suka faru a Kannywood makon jiya

Hakkin mallakar hoto Instagram/realsanidanja
Image caption Ranar Litinin tauraro Sani Danja (dama) ya wallafa hoton ziyarar da suka kai wa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed (tsakiya) tare da amininsa, Yakubu Mohammed (hagu) domin taya shi murnar yin nasara a kotun koli.
Hakkin mallakar hoto Instagram/khadejah_mustapha
Image caption Ranar Laraba Khadija Mustapha ta yi murnar zagayowar ranar haihuwarta, wato birthday
Hakkin mallakar hoto Instagram/Instagram
Image caption ...A ranar ne tauraruwa Rahama Sadau, ta wallafa wannan hoto tare da Adam Zango inda take cewa shi kadai ne "Yariman da na sani" a masana'antar Kannywood.
Hakkin mallakar hoto Instagram/adam_a_zango
Image caption ...washegari Adam Zango ya wallafa hotonsa da matarsa, Safiya, yana mai cewa "Daga ke..." ba kowa ko?
Hakkin mallakar hoto Instagram/@centurymediaacademy
Image caption Ali Nuhu a cikin fim mai suna A Call To Service, wanda aka yi domin wayar da kan masu yi wa kasa hidima a Najeriya
Hakkin mallakar hoto Instagram/falalu_a_dorayi
Image caption Falalu Doraya (hagu) da Nazifi Asnanic suna tattaunawa. Me suke cewa ne?
Hakkin mallakar hoto Instagram/abbaelmustapha1
Image caption Abba Almustapha ya wallafa wannan hoto a shafinsa na Intagram ranar Juma'a inda yake godiya ga Allah bisa samun digiri mai daraja ta biyu
Hakkin mallakar hoto Instagram/nuhuabdullahi
Image caption Mene ne ya yi wa Nuhu Abdullahi dadi, a sanya shi kyakkyalewa da wannan dariya?

Labarai masu alaka